Haɗin gwiwar jami’an tsaro ƙarƙashin ya yi nasarar kama makamai da albarusai da ake zargin an shirya kai wa ’yan ta’adda a Jihar Kogi.
A wata sanarwa da ya fitar, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na jihar, rundunar Hybrid Forces ta ONSA, DSS da kuma Rundunar Sojin Nijeriya ta 12 Brigade.
Rahotannin sirri sun nuna cewa an gano wani shiri na safarar makamai zuwa hannun masu aikata miyagun laifuffuka. Bayan sa ido da aka yi na sama da makonni biyu, jami’an tsaro sun cafke mutum uku a Jihar Sokoto tare da gano hanyar safarar makaman.
Daga cikin makaman da aka kama akwai bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, magazin na AK-47, harsasai 67 na 7.62mm, bindigogi ƙanana guda biyu, harsasai 12 na bindigogin hannu da kuma kayan sojoji. An kuma ƙwace motar Golf 2 da ake amfani da ita wajen jigilar makaman.
Gwamnatin jihar ta ce makaman suna daga cikin yunƙurin da ragowar ’yan ta’adda suke yi na sake ƙarfafa kan su bayan mummunan farmakin da jami’an tsaro suka yi masu, ciki har da kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga Kachalla Battijo.
Ta yaba wa Mai Ba Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, da Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa Kogi ba za ta zama mafakar ’yan ta’adda ba, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da masu aikata miyagun laifuka.







