Allah ya yi wa fitaccen tsohon ɗan damben gargajiya ɗin nan, Alhaji Yahaya Ibrahim Bargaja, wanda aka fi sani da Bagobiri Ɗantcimau, rasuwa bayan fama da rashin lafiya.
Shekarun sa 86 a duniya.
Marigayin ya rasu ne a yau Litinin a garin su na Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda ya shafe wani lokaci yana jinya kafin Allah ya karɓi ran sa.
Ɗanmadamin Birnin Magaji, Alhaji Ibrahim Muhammad, shi ne ya bayyana labarin a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce mariganyin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman damben gargajiya a ƙasar Hausa, inda ya yi fice musamman daga ƙarshen shekarun 1960 zuwa shekarun 1970 da kuma 1980.
Shaharar sa ta kai har fitaccen makaɗin dambe, Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yartsakkuwa, wanda aka fi sani da Gandi Sakkwato, ya yi masa waƙa mai ɗauke da amshin: “Yaƙi sabon Bagobiri, mai kayan hwaɗa.”
Ɗanmadamin ya ce a lokacin da Bagobiri Ɗantcimau yake taka rawar sa a fagen dambe, ya fafata da shahararrun ‘yan dambe da dama, ciki har da Umaru Gundumi na Karime, Arnen Ɓalli, Audu Kure, Lawai Basafce, Maigari Ba-Imani, Ɗankincimi, Ado Ɗankore, Mushe, Gadede, Goto, Kundi da Shagon Wanke, tare da wasu fitattun jarumai da dama.
An gudanar da jana’izar sa a garin Bargaja, inda ya bar iyali, ‘ya’ya da sauran ‘yan’uwa masu yawa.
Ɗanmadami ya ƙara da cewa ko a cikin shekarun sa na ƙarshe, marigayin ya ci gaba da kasancewa cikin harkokin al’adun Hausawa. A watan Afrilu na wannan shekara ta 2026, ya halarci bikin buɗe taron ƙasa kan tarihin rayuwa da waƙoƙin makaɗin dambe Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yartsakkuwa, wanda Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, ta shirya.
A wajen taron, ya sake haɗuwa da tsohon abokin fafatawar sa, Umaru Gundumi.
Masoya da al’ummar dambe sun bayyana rasuwar Bagobiri Ɗantcimau a matsayin babban rashi ga al’adun Hausawa da kuma tarihin damben gargajiya, musamman in aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa wannan wasa na gargajiya.







