Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttaqha Rabe Darma, ya yaba da tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su da ke tafiyar da aikin gina rukunin gidaje na Renewed Hope City a Jihar Kano, yana mai bayyana shi a matsayin hanya mai amfani kuma mai ɗorewa wajen hanzarta samar da gidaje a faɗin ƙasar nan.
Da yake magana yayin ziyarar duba aikin, Ministan ya bayyana cewa ci gaba da duba ayyukan gidajen Gwamnatin Tarayya wani ɓangare ne na ƙoƙarin ma’aikatar wajen sa ido kan yadda ayyukan suke tafiya, magance ƙalubalen aiwatarwa, da kuma gaggauta samar da ingantattun gidaje ga ’yan Nijeriya daidai da Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Darma ya tuna cewa a lokacin taron PPP Housing Summit 2.0 da aka gudanar a Abuja, ya bayyana aniyar sa ta kai ziyarce-ziyarce zuwa wuraren ayyukan gidaje a faɗin ƙasar nan domin ya tantance da kan sa matsayin fiye da gidaje 15,000 da ake ginawa a ƙarƙashin shirye-shiryen gidaje daban-daban na Gwamnatin Tarayya.
A cewar sa, an tsara wannan rangadin duba ayyuka a duk faɗin ƙasar nan ne domin samun bayanai kai-tsaye kan yadda ake aiwatar da ayyukan, gano matsalolin da ke buƙatar sa hannun gwamnati, da kuma sauƙaƙa kammalawa da miƙa gidajen cikin gaggawa ga ’yan Nijeriya da suka cancanta.
Ya bayyana cewa irin waɗannan ziyarce-ziyarcen suna ba da damar tantance sauri da ingancin aikin da ake yi, tattaunawa kai-tsaye da masu haɓaka ayyuka da ’yan kwangila, da tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan bisa ƙa’idoji da jadawalin da aka amince da su.
Ya ce: “Manufar waɗannan bincike-bincike ita ce tabbatar da cewa ayyukan suna tafiya yadda aka tsara su kuma ’yan Nijeriya sun fara cin gajiyar waɗannan shirye-shiryen gidaje cikin gaggawa. Mun himmatu wajen kawar da duk wani cikas da tabbatar da kammalawa da miƙa ayyukan a kan lokaci.”
Darma ya kuma yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya da abokan hulɗar ta daga ɓangaren kamfanoni masu zaman kan su, yana mai cewa tsarin PPP ya nuna yadda za a iya amfani da albarkatun gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su yadda ya kamata wajen rage giɓin gidaje da ƙasar ke fuskanta, tare da ƙarfafa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Ya lura da cewa baya ga samar da matsuguni, aikin Renewed Hope City na Kano ya riga ya fara haifar da manyan harkokin tattalin arziki a yankin ta hanyar samar da ayyuka ga masu sana’o’in hannu, ’yan kwangila, masu samar da kayayyaki, masu sufuri da sauran masu ba da hidima da ke da hannu a aikin ginin.
Ya ce: “Tasirin tattalin arzikin wannan aiki ya wuce gidajen da ake ginawa kawai. Yana samar da ayyukan yi, tallafa wa kasuwancin cikin gida, jawo hannun jari, tare da taimaka wa cigaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yankin.”
Ministan ya bayyana cewa aikin, wanda ya ƙunshi gidaje 1,500 na nau’o’i daban-daban, yana da damar ɗaukar fiye da mazauna 6,000 bisa matsakaicin mutum huɗu a kowace iyali.
Ya jaddada cewa wannan cigaba ba kawai zai samar da ingantattun gidaje masu araha ba ne, har ma zai taimaka wajen samar da al’umma mai ƙarfi, aminci da ɗorewa tare da ingantaccen yanayin rayuwa.
Ya bayyana gamsuwa da saurin aikin da kuma ingancin aikin da ake yi a wurin, tare da kira ga duk masu ruwa da tsaki su ci gaba da jajircewa wajen cimma burin kammala aikin.

Ministan ya sake nanata ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ci gaba da binciko sababbin hanyoyin samar da kuɗaɗen ayyuka da kuma ƙulla dabarun haɗin gwiwa da za su faɗaɗa damar samun gidaje masu araha, ƙarfafa kayayyakin more rayuwa na birane, samar da ayyukan yi, da kuma bunƙasa cigaba mai amfani ga kowa a faɗin ƙasar nan.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane, Badamasi Haiba, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: “Aikin Renewed Hope City na Kano yana ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen gidaje na musamman da Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya take aiwatarwa domin magance matsalar gidaje a Nijeriya, tare da tallafa wa bunƙasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma a ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope.”






