Ana sa ran farashin lemon kwalba zai tashi a Nijeriya kwanan nan domin Majalisar Dattawa ta amince a ranar Laraba da sabon tsarin harajin kayan sha masu ɗauke da sukari.
Majalisar ta kuma amince da kafa wani keɓaɓɓen asusun kuɗi domin ƙarfafa shirye-shiryen kula da lafiyar al’umma a faɗin ƙasar.
Majalisar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne da nufin rage yawaitar cututtukan da ba sa yaɗuwa daga mutum zuwa mutum (NCDs).
An cimma wannan matsaya ne bayan nazari da amincewa da rahoton Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Kuɗi da Kwastam, Harajin Kaya da Sauran su kan Ƙudirin Gyaran Dokar Kwastam da Harajin Kaya da Sauran su, yayin zaman majalisar.
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗi, Sanata Sani Musa, shi ne ya gabatar da rahoton.
Ya bayyana cewa a ƙarƙashin sabon tsarin, za a soke harajin Naira 10 kan kowace lita ta kayan sha masu ɗauke da sukari da ake biya a yanzu, a maye gurbin sa da haraji na kaso-kaso bisa farashin sayarwa, wanda Ministan Kuɗi zai tantance daidai da ƙa’idojin duniya.
Musa ya ce harajin da ake karɓa a matsayin adadi ɗaya a yanzu ya ragu ƙwarai sakamakon hauhawar farashi, kuma ba ya da tasirin da zai hana yawan shan irin waɗannan kayan sha ko kuma samar da isasshen kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Ya nuna damuwa kan yadda cututtukan da ba sa yaɗuwa kamar ciwon sukari, ƙiba, hawan jini da cututtukan zuciya da jijiyoyin jini suke ƙaruwa, waɗanda ake danganta su da yawan amfani da sukari da kuma rashin kyawawan halayen cin abinci.
Ya kuma lura da cewa har yanzu tsarin kiwon lafiya na Nijeriya yana fama da ƙarancin kuɗaɗen tallafi, kuma ya dogara sosai da kuɗin da marasa lafiya ke biya daga aljihun su, lamarin da ke jefa mutane da dama cikin matsin tattalin arziki tare da taƙaita musu damar samun kulawar lafiya.
Daga nan Majalisar Dattawa ta umurci Ministan Kuɗi da ya tsara tsarin harajin da ya dace da ƙa’idojin duniya tare da tabbatar da cewa aiwatar da shi ya yi daidai da manufofin Nijeriya na kiwon lafiya da tattalin arziki.
Majalisar ta kuma ba da shawarar ƙarfafa hanyoyin tabbatar da tattara harajin yadda ya kamata, ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma ɗaukar ƙarin matakai kamar kamfen ɗin wayar da kan jama’a kan ingantaccen abinci mai gina jiki.






