Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai a Jaridu, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa an ɗauki masu tsaron daji (forest guards) a jihohi 10 na Arewa, sannan ana shirin ɗauka a wasu jihohin.
Abdulaziz ya yi tsokacin ne a yayin da wasu suke saukar Gwamnatin Tarayya kan za ta ɗauki masu tsaron daji a jihohi Kudu, musamman a Jihar Oyo.
Ya ce: “Tun jiya da jaridu suka fara ba da labarin aniyar ɗaukar masu tsaron daji (Forest Guards) guda 1,000 a Jihar Oyo sakamakon kidnapping da aka yi kwanaki na lura wasu mutanen mu na Arewa a Social Media suna ƙorafi ko shaguɓen cewa ‘an taɓa ‘yan gata’.
“A ganin su, wannan abu ne kawai za a yi domin Yarabawa saboda matsalar tsaro ta shafe su. To ba haka ba ne.
“A yanzu haka akwai jihohi 10 da aka kafa rundunar Forest Guards da kuma jihohi duk a Arewa. Kuma kowanne an ɗauki mutum kimanin 1,000 ɗin ne.”
Abdulaziz ya lissafa jihohin kamar haka: Borno, Yobe, Adamawa, Kwara, da Sokoto. Sauran su ne Kebbi, Neja, Filato, da Binuwai.
Haka kuma ya bayyana cewa jihohin da suke kan hanyar samun masu tsaron dajin su ne: Kaduna, Edo, Kogi da Bauchi.
Idan an tuna, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin a ɗauki masu tsaron daji mutum dubu a Jihar Oyo sakamakon sace ɗalibai da wani malamin su da ‘yan ta’adda suka yi.






