• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Hajjin bana: NAHCON ta shawarci mahajjata su sayi dabbobin hadaya ta cibiyoyin da aka amince da su kaɗai

Wakilin Mu by Wakilin Mu
May 25, 2026
in Labarai
A A
0
Hajjin bana: NAHCON ta shawarci mahajjata su sayi dabbobin hadaya ta cibiyoyin da aka amince da su kaɗai
Wata jami'ar Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) tana yi wa alhazai bayani a masaukin su a Saudiyya

Wata jami'ar Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) tana yi wa alhazai bayani a masaukin su a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta yi kira ga dukkan maniyyatan Nijeriya da ke gudanar da aikin Hajjin bana da su tabbatar sun sayi dabbobin hadaya ta hanyar dandalin Nusuk Masar ko kuma cibiyoyin sayarwa da Hukumar Kula da Ayyukan Hadaya da Adahi ta Masarautar Saudiyya ta amince da su.

Hukumar ta jaddada cewa bai kamata mahajjata su yi hulɗa da mutane ko ƙungiyoyin da ba su da izini wajen saye, talla, ko gudanar da duk wani aiki da ya shafi Hadaya da Adahi ba.

NAHCON ta bayyana cewa wannan mataki an ɗauke shi ne domin kare mahajjata daga zamba, damfara da sauran hanyoyin cutarwa, tare da tabbatar da cewa an kiyaye haƙƙoƙin su a lokacin gudanar da ibadun Hajji.

Hukumar ta kuma buƙaci mahajjatan da su yi amfani da hanyoyin da aka amince da su kawai domin tabbatar da cewa an gudanar da ibadar Hadaya da Adahi yadda Shari’ar Musulunci ta tanada tare da bin dokoki da ƙa’idojin Masarautar Saudiyya.

Haka zalika, an umurci Hukumomi da Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, Hukumomin Hajji da Umrah, Kwamitocin Alhazai da kuma Kamfanonin Shirya Hajji da su wayar da kan mahajjata tare da tabbatar da cikakken bin wannan umurnin.

NAHCON ta yi addu’ar Allah ya karɓi ibadun mahajjata baki ɗaya, ya ba su Hajji Mabrur, ya kuma dawo da su gida lafiya.

Tags: alhazaihadayaHajji2026NAHCONSaudiyya
Previous Post

Hukumar NSCDC ta rufe Inner Galaxy Steel, kamfanonin ‘yan Chana masu satar ƙarafa suna narkarwa domin sayarwa

Next Post

Gwamnatin Katsina ta ce an dakatar da wanda ake zargi da jagorancin ƙungiyar kidinafas tun kafin yunƙurin sa na neman zama ɗan majalisar dokoki a matsayin SSA

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamnatin Katsina ta ce an dakatar da wanda ake zargi da jagorancin ƙungiyar kidinafas tun kafin yunƙurin sa na neman zama ɗan majalisar dokoki a matsayin SSA

Gwamnatin Katsina ta ce an dakatar da wanda ake zargi da jagorancin ƙungiyar kidinafas tun kafin yunƙurin sa na neman zama ɗan majalisar dokoki a matsayin SSA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!