• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Gwamnatin Katsina ta ce an dakatar da wanda ake zargi da jagorancin ƙungiyar kidinafas tun kafin yunƙurin sa na neman zama ɗan majalisar dokoki a matsayin SSA

ALI KANO by ALI KANO
May 25, 2026
in Tsaro
A A
0
Gwamnatin Katsina ta ce an dakatar da wanda ake zargi da jagorancin ƙungiyar kidinafas tun kafin yunƙurin sa na neman zama ɗan majalisar dokoki a matsayin SSA
Nura Aliyu Garwa

Nura Aliyu Garwa

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce tun kafin bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar zama ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari, tuni ta dakatar da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar kan Harkokin Cigaban Al’umma, Nura Aliyu Garwa, bisa zargin sa da kasancewa jagoran wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a jihar.

Ana zargin Garwa da hannu a sace wani yaro ɗan shekara takwas a unguwar Sardauna Estate da ke cikin birnin Katsina, inda rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana shi tare da wasu da ake zargi da aikata laifin.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa gwamnatin jihar ta dakatar da Garwa ne saboda “hannun sa a karkatar da kayan tallafi da aka tanada domin raba wa al’ummomin Ƙaramar Hukumar Batsari a ƙarƙashin Shirin Cigaban Al’umma na gwamnatin jihar.”

Ya ce Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana ayyukan wannan ƙungiya a matsayin abin takaici, musamman ganin cewa lamarin ya shafi mutum mai matsayi wanda har ya taɓa neman kujerar zama ɗan majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya yaba wa rundunar ’yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaro bisa jajircewar su wajen tabbatar da tsaron jihar.

Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su mara wa ƙoƙarin gwamnati baya ta hanyar bai wa hukumomin tsaro bayanai da kuma kai rahoton duk wani abu da suke zargin ba daidai ba ne.

Tags: Bala Salisu ZangoGwamna Dikko Umar RaɗɗaKatsinamasu garkuwaNura Aliyu Garwatsaro
Previous Post

Hajjin bana: NAHCON ta shawarci mahajjata su sayi dabbobin hadaya ta cibiyoyin da aka amince da su kaɗai

Next Post

Nijeriya ta ayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Sallah

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Nijeriya ta ayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Sallah

Nijeriya ta ayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Sallah

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!