• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Hukumar NSCDC ta rufe Inner Galaxy Steel, kamfanonin ‘yan Chana masu satar ƙarafa suna narkarwa domin sayarwa

Kamfanonin suna da tsarin lalatawa da sace muhimman kayayyakin more rayuwa na Nijeriya na biliyoyin naira

ALI KANO by ALI KANO
May 25, 2026
in Labarai
A A
0
Hukumar NSCDC ta rufe Inner Galaxy Steel, kamfanonin ‘yan Chana masu satar ƙarafa suna narkarwa domin sayarwa
Wani jami'an tsaro yana gadin kayan kamfanin Inner Galaxy Steel da ake zargin na sata ne

Wani jami'an tsaro yana gadin kayan kamfanin Inner Galaxy Steel da ake zargin na sata ne

Hukumar Tsaro da Kariya ta Farar Hula ta Nijeriya (NSCDC) ta samu cikakken umurnin kotu na rufe dukkan rassan wasu kamfanonin ‘yan Chana masu suna Inner Galaxy Steel Company da Jiuxing Integrity Industrial Ltd a faɗin ƙasar nan sakamakon ta’annatin da suke yi wa tattalin arzikin ƙasar nan ta hanyar satar ƙarafa.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙasa na NSCDC, Afolabi Babawale, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: “Wannan mataki na nuna ƙara tsaurara matakin Gwamnatin Tarayya kan ta’ammali da ta’addancin tattalin arziki, satar kayayyakin more rayuwa, da kuma zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuɗi.”

Mutanen da ake zargi da alaƙa da wannan ƙungiya suna fuskantar manyan tuhume-tuhume na laifuffuka da suka haɗa da:

  • Haɗa baki wajen aikata babban laifi da sata,
  • Ganganci wajen jefa lafiyar matafiya ta jirgin ƙasa cikin haɗari
  • Hana aiki, lalata da jikkata kayayyakin layin dogo
  • Gaza bayar da rahoto ko bayanai ga jami’in gwamnati
  • Karɓa da taimakawa wajen ɓoye kayan sata da aka samu ta haramtacciyar hanya
  • Taimakawa da ba da kuɗin tallafi ga ƙungiyoyin ta’addanci domin aikata ayyukan ta’addanci
  • Aiwatar da umurnin kotu da ƙwato kadarori

Bayan sun samu takardun bincike da umurnin kotu, jami’an rundunar Commandant General’s Special Intelligence Squad (CG’S SIS) sun kai samame cibiyar kamfanin da ke Birnin Yero, Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna inda suka ƙwato dukkan kayayyakin layin dogo da aka sata aka sayar wa da kamfanin, ciki har da railway sleepers da layukan dogo.

Wasu muhimman ƙarafa da NSCDC ta kama a kamfanin Inner Galaxy Steel Limited

An tara su tare da miƙa su ga Hukumar Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC) domin amfani da su a matsayin muhimman hujjoji a shari’a.

Bayanai daga furucin ma’aikatan da aka kama sun nuna cewa akwai wata hanyar safarar kayayyaki da aka tsara, inda ake kai kayan more rayuwar ƙasa da aka lalata zuwa hedikwatar kamfanin da ke Aba da sauran rassan sa domin narkar da su. Daga nan kuma ana sarrafa ƙarfen da aka sace zuwa kayayyakin kasuwanci kamar ƙusoshi da kwanon rufi.

Sakamakon wannan bincike, an faɗaɗa umurnin rufe kamfanonin da gudanar da bincike zuwa:

  • Hedikwatar Inner Galaxy Steel Company / Jiuxing Integrity Industrial Ltd da ke ƙauyen Ahala Ukwa, Umuahala Community, Obuzor Ukwu, Ukwa West LGA, Jihar Abia)
  • Cibiyar Arewa na Inner Galaxy Steel Company da ke Tashar Rawayya, Gusau, Jihar Zamfara
  • Dukkan sauran rassan kamfanonin da ƙananan kamfanonin su a faɗin Nijeriya

NSCDC ta gayyaci ’yan ƙasar Chaina da ke da hannu wajen tafiyar da wannan katafaren kamfani a rubuce domin amsa tambayoyi, amma sun ƙi zuwa.

NSCDC ta gayyaci ’yan ƙasar Chaina da ke da hannu wajen tafiyar da wannan katafaren kamfani a rubuce domin amsa tambayoyi, amma sun ƙi zuwa.

Babban Kwamandan NSCDC na ƙasa, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya bayar da kakkausan umurni ga kwamandan da ke kula da rundunar CG’S SIS, Mista Appollos Ɗandaura, domin tabbatar da jami’ai sun gudanar da wannan aiki cikin ƙwarewa da jajircewa.

Ya ce: “Duk wanda aka samu da laifi wajen wannan al’amari da zubar da dukiyar al’ummar ƙasa zai fuskanci cikakken hukuncin doka. NSCDC tana ci gaba da jajircewa wajen rage lalata kayayyakin more rayuwa zuwa mafi ƙanƙanta.”

Tarin ƙarafa a kamfanin wanda ake zargin kayan sata ne

NSCDC ta bayyana matuƙar godiyar ta ga ɓangaren shari’a bisa gaggawar bayar da waɗannan umurnin doka, wanda ya taimaka wajen hana katsalandan ga muhimman hujjoji.

Haka kuma, hukumar ta yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa muhimmiyar gudunmawar su wajen fallasa waɗannan laifuffukan tattalin arziki da tabbatar da gaskiya da riƙon amana ga jama’a.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da haɗa kai da hukumar ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin kawo ƙarshen satar kayayyakin more rayuwa.

Jami’an NSCDC a kamfanin Inner Galaxy Steel Limited
Tags: Inner Galaxy SteelNSCDCsataƙarafa
Previous Post

2027: Tinubu ya zama ɗan takarar APC tare da alƙawarin ƙarfafa sauye-sauye

Next Post

Hajjin bana: NAHCON ta shawarci mahajjata su sayi dabbobin hadaya ta cibiyoyin da aka amince da su kaɗai

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Hajjin bana: NAHCON ta shawarci mahajjata su sayi dabbobin hadaya ta cibiyoyin da aka amince da su kaɗai

Hajjin bana: NAHCON ta shawarci mahajjata su sayi dabbobin hadaya ta cibiyoyin da aka amince da su kaɗai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!