Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Laraba da kuma Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Sallah (Eid ul-Adha).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya ba da sanarwar hakan.
Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa: “Wannan ayyana hutun yana nuna irin girmamawa mai zurfi da Gwamnatin Tarayya take yi ga addini da zukatan miliyoyin Musulman Nijeriya da ke haɗuwa da al’ummar Musulmi ta duniya wajen gudanar da wannan ibada mai alfarma.”
Ta ce ministan ya miƙa saƙon taya murna na gwamnati ga ɗaukacin al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma waɗanda suke ƙasashen waje.
Ajani ta ƙara da cewa: “Eid ul-Adha biki ne mai matuƙar muhimmanci a ɓangaren ibada, wanda ya ginu kan darussan sadaukarwa, biyayya ga Allah, da tausayi ga ‘yan’uwa.”
Gwamnatin ta buƙaci ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a da yin tunani mai zurfi, tare da neman shiriyar Ubangiji ga ƙasa yayin da take ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da wadata ga kowane ɗan ƙasa.
“Cikin ruhin ‘yan’uwantaka, mutuntaka ta bai ɗaya, da haɗin kan ƙasa, Gwamnatin Tarayya tana yi wa ɗaukacin Musulmai fatan bikin cikin lumana, albarka, da farin ciki,” inji ta.







