• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙungiyar al’ummar Birnin-Gwari ta yaba wa Gwamna Uba Sani kan aikin gyaran hanya na ₦178 biliyan da kuma dawo da zaman lafiya

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 1, 2026
in Labarai
A A
0
Ilimin ‘ya mace: Fiye da ‘yan mata 40,000 a Kaduna sun amfana da shirin koyon dabarun rayuwa na Gwamna Uba Sani
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna

Ƙungiyar Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance ta bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa samun amincewar Gwamnatin Tarayya na fara sake gina hanyar Mando–Kaduna zuwa Birnin-Gwari mai tsawon kilomita 122, wanda kuɗin sa ya kai naira biliyan 178, wani muhimmin sashe na babbar hanyar Kaduna zuwa Legas.

A wata sanarwa da shugaban ta, Ibrahim Abubakar Nagwari, ya fitar a ranar Juma’a, ƙungiyar ta tuna da alƙawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a lokacin da ya kai ziyara Birnin-Gwari kafin babban zaɓen 2023, tana mai cewa: “Yanzu, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani mai ma’ana, ana cika wannan alƙawari. Wannan hanya za ta inganta haɗin kai, ƙarfafa ayyukan tsaro, sauƙaƙa ayyukan noma, tare da dawo da amincewa ga al’ummomin da suka daɗe suna fama da wariya.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Muna kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna kan gina hanyar Bagoma zuwa Gagumi mai tsawon kilomita 36 a yammacin ƙasar Birnin-Gwari, da kuma kafa kasuwar shanu ta zamani da mayanka a garin Birnin-Gwari.

“Waɗannan ayyuka ba wai kawai tsare-tsare na ɗan lokaci ba ne, illa sun zama ginshiƙai na dindindin da za su tabbatar da makoma mai wadata, tsaro, da haɗin kai ga al’ummar mu.”

“Muna matuƙar farin ciki da jajircewar Gwamna Uba Sani wajen wanzar da zaman lafiya mai ɗorewa bayan sama da shekaru goma sha biyar na zubar da jini, garkuwa da mutane, da fashi ta hanyar tsarin Kaduna Peace Model wanda al’umma ke jagoranta.

“An ga sakamakon a zahiri: cikin watanni goma sha takwas da suka gabata, matafiya sun riƙa zirga-zirga cikin kwanciyar hankali a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba.

“Ayyukan noma sun samu gagarumin cigaba, inda aka share sababbin gonaki domin noman bana.

“Gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna cikakkiyar jajircewa wajen aiwatar da waɗannan ayyuka yadda ya kamata. Muna gode wa Shugaban Ƙasa bisa tsayin daka da ya yi ga Jihar Kaduna da kuma cigaban ƙasa baki ɗaya cikin adalci.

“Muna kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta ci gaba da ƙarfafa tsarin Kaduna Peace Model ta hanyar ci gaba da hulɗa mai inganci da al’ummomi domin sulhu, warkar da raunuka, da bunƙasa cigaba.”

Tags: Gwamna Uba SanihanyoyiKaduna Peace Model
Previous Post

Gwamna Uba Sani ya gode wa Tinubu kan kwangilolin ayyuka na sama da Naira tiriliyan 1 da biliyan 178 a Jihar Kaduna

Next Post

Shugaban Ƙasa ya taya Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris Malagi murnar cika shekaru 60

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Shugaban Ƙasa ya taya Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris Malagi murnar cika shekaru 60

Shugaban Ƙasa ya taya Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris Malagi murnar cika shekaru 60

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!