Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, murnar cikar sa shekaru 60 da haihuwa, wanda ya kama ranar 2 ga Mayu, 2026.
A saƙon, wanda ya rattaba wa hannu da kan sa, Shugaban Ƙasa ya ce: “Mohammed ƙwararren mai sadarwa ne, ƙwararren masani a harkar hulɗa da jama’a, kuma jagora a fannin kafafen yaɗa labarai wanda ya kawo ƙwarewa, amana da ɗaukar nauyi a harkar sadarwar gwamnati a cikin wannan mulki namu.
“Sunan sa ya riga ya yi masa shaida. Ya kasance a sahun gaba a masana’antar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a a matsayin wanda ya kafa kuma mai wallafa jaridar Blueprint, haka kuma shugaban wani kamfanin hulɗa da jama’a da ya cimma nasara, sannan gidan rediyo.
“Matsayin da ya riƙe na Babban Sakataren Ƙungiyar Masu Mallakar Jaridu ta Nijeriya (NPAN) kafin naɗin sa ya nuna shi a matsayin mai kishin ƙasa kuma abokin aiki mai muhimmanci wajen gina ƙasa.
“Ina yaba wa Mohammed bisa ƙwazo, basira da jajircewar sa wajen isar da nasarori, manufofi da shirye-shiryen wannan gwamnati tamu.
“Ya kasance mai tsayawa tsayin daka wajen yaɗa saƙon Sabon Fata a faɗin ƙasar nan, kuma ina ƙarfafa masa gwiwa da ya ci gaba da kyakkyawan aikin da yake yi.
“Yayin da Mohammed yake bikin wannan muhimmiyar ranar haihuwa, ina tare da iyalan sa da abokan sa wajen yi masa fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya da ƙarfi yayin da yake ci gaba da hidimta wa ƙasa.
“Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Nijeriya, Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya, 1 ga Mayu, 2026.”







