• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Minista ya lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu ga ‘yan jarida na duniya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
April 23, 2026
in Labarai
A A
0
Minista ya lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu ga ‘yan jarida na duniya
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da sauran jami'ai a wurin taron

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da sauran jami'ai a wurin taron

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya ta shiga wani sabon babi na gyara da ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta buƙaci kafofin yaɗa labarai na duniya da su riƙa rahoton gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa ta musamman da wakilan gidajen jaridun ƙasashen waje a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa a shekarar 2025, tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.87 cikin ɗari, wanda hakan ke nuna cewa ci gaban tattalin arzikin ya fi ƙaruwar yawan jama’a sauri a karon farko cikin kusan shekara goma.

A cewarsa, cire tallafin man fetur da gyara tsarin musayar kuɗi sun taimaka kwarai wajen tara kuɗaɗen da ake amfani da su yanzu wajen samar da manyan ayyuka da inganta rayuwar al’umma.

Alhaji Mohammed Idris ya jero wasu daga cikin muhimman nasarorin da aka samu, waɗanda suka haɗa da:

• Samar da lamunin karatu ga ɗalibai ta hanyar asusun NELFUND.

• Inganta harkar tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri da leken asiri.

• Yunkurin kafa ’yan sandan jihohi domin bai wa hukumomin gida yancin cin gashin kansu.

• Zuba jari a fannin noma da fasahar zamani domin samar wa matasa ayyukan yi.

A nasa jawabin, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa Nijeriya ta fita daga yanayin fargaba, yanzu tana matakin tabbatar da cewa al’umma sun fara jin daɗin waɗannan gyare-gyare a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Haka ita ma Ministar Masana’antu da Kasuwanci, Dr. Jumoke Oduwole, ta jaddada cewa Nijeriya ba kawai tana binsu a bayan Afirka ba ne, tana kokarin zama jagora ne a fannin ciniki da masana’antu a faɗin nahiyar.

Minista Idris ya rufe jawabin nasa da kira ga ’yan jaridun duniya da su riƙa bayyana gaskiya game da Nijeriya.

Ya ce: “Muna son a riƙa bayyana nasarorinmu da kuma ƙalubalen da muke fuskanta duka tare, domin hakan ne kawai zai nuna ainihin hoton Nijeriya.”

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Bayo Onanuga da Sunday Dare da kuma Abdulaziz Abdulaziz, waɗanda duka ke tallafa wa shugaban ƙasa a fannin yaɗa labarai da sadarwa.

Previous Post

Abba Yusuf ya tura wa majalisa sunan Garo ta tantance shi don zama Mataimakin Gwamna

Next Post

Maiɗakin Tinubu, ta ƙaddamar da shirin ECoN, tana so a mayar da hankali kan masana’antu

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Maiɗakin Tinubu, ta ƙaddamar da shirin ECoN, tana so a mayar da hankali kan masana’antu

Maiɗakin Tinubu, ta ƙaddamar da shirin ECoN, tana so a mayar da hankali kan masana’antu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!