• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Maiɗakin Tinubu, ta ƙaddamar da shirin ECoN, tana so a mayar da hankali kan masana’antu

Wakilin Mu by Wakilin Mu
April 23, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Maiɗakin Tinubu, ta ƙaddamar da shirin ECoN, tana so a mayar da hankali kan masana’antu
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tana ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken Energise Commercialisation Now (ECoN) a birnin Kano yau Alhamis

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tana ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken Energise Commercialisation Now (ECoN) a birnin Kano yau Alhamis

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken Energise Commercialisation Now (ECoN) a birnin Kano yau Alhamis, inda ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina tsayawa ga tunanin ayyuka kawai, maimakon haka su duƙufa wajen gina masana’antu.

Da take jawabi a wajen taron, Sanata Oluremi ta bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce mai cike da fasaha da hazaka, inda kullum ake samun sabbin ra’ayoyi daga jami’oi da cibiyoyin fasaha, amma abin takaicin shi ne yawancin waɗannan ra’ayoyin ba sa komawa ayyukan da za su amfani al’umma a aikace.

Manufar shirin ECoN

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce: “Wannan shiri na ECoN wani gagarumin mataki ne na dinke barakar da ke tsakanin tunanin ayyuka da aiwatar da su. Muna son samar da yanayi inda za a tallafa wa ra’ayoyin matasa da masu bincike domin su zama manyan masana’antu.”

Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka ƙwarai wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki, da kuma sanya Nijeriya takara da sauran ƙasashen duniya a fagen kasuwanci da fasaha. Ta kuma nanata cewa mata da matasa ne za su kasance a gaba-gaba a dukkan shirye-shiryen gwamnati.

A nasa jawabin, Ministan Fasaha da Kimiyya, Dr. Kingsley Udeh, ya ce an samar da ECoN ne domin magance tsohuwar matsalar nan ta Nijeriya, inda ake bincike mai kyau amma ba a kai shi kasuwa domin ya zama kuɗi.

A cewar sa, bincike da dama na nan sun maƙale a ɗakunan gwaje-gwaje saboda rashin kuɗi ko kuma rashin hanyar kai su ga masu saye.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin daɗin sa kan yadda aka zaɓi Kano domin ƙaddamar da wannan shiri na ƙasa da kuma na shiyyar Arewa maso Yamma. Ya bayyana cewa Kano ta riga ta fara shiri ta hanyar inganta ilimin kimiyya da fasaha da kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa na zamani (ICT).

Shi ma Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, wanda ya yi magana a madadin Gwamnonin Arewa maso Yamma, ya lashi takobin cewa gwamnonin shiyyar za su ba da cikakken haɗin kai. Ya bayyana cewa Jihar Jigawa ma na shirin kafa “Garuruwan Fasaha” (Technology Village) domin bunƙasa harkar bincike da jan hankalin masu zuba jari.

Previous Post

Minista ya lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu ga ‘yan jarida na duniya

Next Post

Dalla-Dalla: Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara ta intanet, masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗaɗen ajiyar kwastomomin bankuna

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Dalla-Dalla: Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara ta intanet, masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗaɗen ajiyar kwastomomin bankuna

Dalla-Dalla: Yadda CBN ya bankaɗo 'yan damfara ta intanet, masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗaɗen ajiyar kwastomomin bankuna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!