• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Sabon tsarin leƙen asiri da bayanan sirri sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Wakilin Mu by Wakilin Mu
April 23, 2026
in Labarai
A A
0
Sabon tsarin leƙen asiri da bayanan sirri sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris
Hagu zuwa dama: Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, Mista Ogbodo Chinasa Nnam; Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz; Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris; Ministan Kuɗi kuma Ministan Daidaita Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga; da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Hulɗar Jama’a da Wayar da Kai, Mista Sunday Dare, yayin wani taron bayani da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ya yi da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje, wanda aka gudanar a ranar 23 ga Afrilu, 2026, a Abuja. (Hoto: Khalid Ahmed/FMINO)

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sabon salon da ta ɓullo da shi na yin amfani da bayanan sirri da leƙen asiri wajen yaƙar rashin tsaro, ya fara samar da gagarumar nasara a faɗin ƙasar nan.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a Abuja, lokacin da yake tattaunawa da wakilan kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje.

Ministan ya bayyana cewa a yanzu gwamnati ta canza sheƙa daga jiran sai ɗan bindiga ya kawo hari kafin a mayar da martani, zuwa ga yin amfani da bayanan sirri domin daƙile harin tun kafin ya auku.

Ya ce an samu kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin sojoji, ’yan sanda, DSS da kuma hukumomin leƙen asiri na ƙasa.

A cewar sa, wannan haɗin gwiwar ne ya kai ga kamo shahararren kwamandan ƙungiyar ISWAP, Mahmoud, da babban hadimin sa, waɗanda ma hukumomin ƙasashen waje irin su Amurka ke nema ido rufe.

Idris ya buga misali da hanyar mota da ta jirgin ƙasa ta Abuja zuwa Kaduna, wadda a baya take matsayin sahun gaba a wuraren da ake garkuwa da mutane.

Ya ce: “Ina gaya muku, ni kai na jiya na dawo daga Kaduna ta wannan hanyar. A baya, ba wanda zai bi ta ba tare da ya yi tambaya ba, amma yanzu hakan ta kau. Hanyar ta samu lafiya sakamakon tura dakaru na musamman da kuma haɗin gwiwar jami’an tsaro.”

Game da batun kafa ’yan sandan jihohi, Ministan ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu da Majalisar Ƙasa sun riga sun fara shirin yi wa kundin tsarin mulki garambawul. Ya ce ana sa ran kammala komai nan da ƙarshen shekarar 2026 bayan an tuntuɓi masu ruwa da tsaki a faɗin Nijeriya.

Ya bayyana cewa an samar da matakan kariya a cikin dokar domin tabbatar da cewa ba a yi amfani da ’yan sandan jihohin wajen cin zarafin mutane ba.

Haka kuma, Ministan ya taɓo batun ikon ƙananan hukumomi, inda ya ce gwamnati ta fara tura masu da kuɗaɗen su kai-tsaye daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) kamar yadda Kotun Ƙoli ta bayar da umarni. Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da tsaro a matakin farko na rayuwar talakawa.

A nasa jawabin, Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya buƙaci ’yan jaridun ƙasashen waje da su riƙa yin adalci a rahotannin su.

Ya soki yadda wasu ke saurin bayar da labarin hare-hare amma su yi gum da baki lokacin da sojoji suka yi nasarar kashe ’yan ta’adda.

Previous Post

Hattara da ‘yan dandatsa! CBN ya yi kakkausan gargaɗin yin kaffa-kaffa da masu yaɗa saƙonnin zamba da ƙoƙarin kutse ta intanet

Next Post

Me ya sa har yanzu ake ciwo bashi bayan Tinubu ya cire tallafin mai? – Sarki Sanusi

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Me ya sa har yanzu ake ciwo bashi bayan Tinubu ya cire tallafin mai? – Sarki Sanusi

Me ya sa har yanzu ake ciwo bashi bayan Tinubu ya cire tallafin mai? - Sarki Sanusi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!