• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hattara da ‘yan dandatsa! CBN ya yi kakkausan gargaɗin yin kaffa-kaffa da masu yaɗa saƙonnin zamba da ƙoƙarin kutse ta intanet

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 23, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Hattara da ‘yan dandatsa! CBN ya yi kakkausan gargaɗin yin kaffa-kaffa da masu yaɗa saƙonnin zamba da ƙoƙarin kutse ta intanet

 

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gargaɗi kan yawaitar saƙonnin zamba da suka ƙunshi imel sauran hanyoyin sadarwa ta yanar gizo na bogi, inda gargaɗin ya bayyana cewa ana zargin masu aikata laifukan yanar gizo suna ƙoƙarin kutsawa cikin tsarin tsaro tare da yaudarar jama’a.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Talata, wanda A Daraktar Sadarwa ta CBN, Hakama Sidi Ali ta sanya wa hannu, CBN ya bayyana cewa waɗannan saƙonnin bogi suna ɗauke da ƙarairayi game da shugabancin bankin, bayar da lasisi, da manufofin sa.

Sanarwar ta ce masu aikata wannan damfara suna amfani da bayanan yaudara domin jan hankalin mutane su danna hanyoyin shiga manhajoji (links) masu haɗari, wanda zai iya ba su damar shiga asusun ajiyar kuɗin mutum, ba tare da izini ba.

Sanarwar ta ce: “CBN na sanar da jama’a cewa ana yaɗa saƙonnin bogi, imel, da hanyoyin sadarwa ta yanar gizo waɗanda ake ƙoƙarin nuna cewa sun fito daga CBN ko suna da alaƙa da shi, domin yaudarar jama’a.

“Waɗannan saƙonnin bogi suna ƙarfafa masu karɓa su danna hanyar shiga wata manhaja, suna yaɗa ƙarya game da shugabancin bankin, bayar da lasisi, da manufofi, kuma manufar su ita ce kutse cikin asusun ajiyar kuɗaɗen jama’a.”

CBN ya jaddada cewa shafin yanar gizon hukuma na bankin shi ne www.cbn.gov.ng.

Yana gargaɗin jama’a da kada su danna links ko su bayar da bayanan su na sirri a shafukan da ake zargi.

Bankin ya kuma shawarci jama’a da su tabbatar da sahihancin duk wata sanarwa daga CBN ta hanyar duba shafin yanar gizon hukuma ko kuma kafofin watsa labarai da aka amince da su.

Haka kuma, CBN ya buƙaci jama’a su kai rahoton duk wani shafi, imel, ko saƙon bogi ga hukumomin tsaro.

Babban bankin ya sake jaddada ƙudirin sa na kare tsarin kuɗi na Nijeriya tare da ƙarfafa matakan tsaron yanar gizo, tare da haɗin gwiwa da hukumomin da suka dace domin kare jama’a daga damfara ta hanyoyin sadarwar zamani, wato dijital.

Previous Post

Dalla-Dalla: Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara ta intanet, masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗaɗen ajiyar kwastomomin bankuna

Next Post

Sabon tsarin leƙen asiri da bayanan sirri sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Sabon tsarin leƙen asiri da bayanan sirri sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Sabon tsarin leƙen asiri da bayanan sirri sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!