Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da manyan jami’an gwamnati da tawagar membobin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a ziyarar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da al’ummar Nijeriya cewa gwamnatin sa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gina ƙasa mai ɗorewa, zaman lafiya, da wadata.
Ya bayyana hakan ne a ranar yau lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar membobin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Tinubu ya bayyana cewa tsarin siyasa da tattalin arzikin da suka daɗe suna dakushe ci gaban ‘yan ƙasa, yanzu ana musanya su da sababbin tsare-tsare da za su ba kowa damar cin moriyar arzikin ƙasa.
Ya kuma sha alwashin ci gaba da aiwatar da garambawul ɗin da nufin samar wa da talakawa da marasa ƙarfi guraben ayyukan yi da sauƙin rayuwa.
Ya ce: “Kuna wakiltar lamirin al’ummar da ke son kakkaɓe sarƙar talauci da yanke ƙauna.”

Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da kada su yarda da kalaman ɓata suna na ‘yan hamayya, inda ya ce idan ma ba su ganin ayyukan hanyoyi da gadoji da ake yi, to za a samar masu da gilashin gani don su gani da kyau.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda
Akwai kuma gwamnoni da suka haɗa da na Yobe, Gombe, Kebbi, Ebonyi, Delta, Kogi, Ekiti, Binuwai, Taraba, Edo, da Kaduna.
Tsofaffin gwamnoni da shugabannin majalisa kamar su Aminu Bello Masari, Ifeanyi Okowa, Tanko Al-Makura, da Anyim Pius Anyim su ma sun halarta.
A nasa jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya yaba wa shugaban bisa ƙarfin halin aiwatar da sauye-sauyen da wasu shugabannin na baya suka kasa yi, musamman batun cire tallafin mai da haɗe farashin canjin kuɗi.
Masari ya tabbatar wa da shugaban cewa jiga-jigan siyasar shiyyar Arewa-maso-yamma suna bayan sa ɗari bisa ɗari, kuma za su zagaya don duba ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke yi a shiyyar domin wayar da kan jama’a.
Daga ƙarshe, Tinubu ya buƙaci membobin ƙungiyar da su ci gaba da isar da saƙon fatan alheri ga jama’a a matakin gundumomi da ƙauyuka, yana mai jaddada cewa “Nijeriya tana hannun amintattu.”







