• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotu ta bayar da belin N200m ga Nasir El-Rufai, amma za a ci gaba da tsare shi har sai …

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
April 16, 2026
in Labarai
A A
0
Kotu ta bayar da belin N200m ga Nasir El-Rufai, amma za a ci gaba da tsare shi har sai …
Malam Nasir El-Rufa'i

Malam Nasir El-Rufa'i

Mai Shari’a Rilwan Aikawa na Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Kaduna ya bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai.

Kotun ta kuma bayar da umurni cewa tsohon gwamnan zai ci gaba da kasancewa a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, wato Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC), har sai an cika dukkan sharuɗɗan  beli.

Kotun ta yanke cewa za a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a hannun ICPC har sai an cika dukkan sharuɗɗan  beli gaba ɗaya.

A matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan, dole masu tsaya masa su ajiye fasfo ɗin su a kotu.

Alƙalin ya kuma umurci cewa dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya masa ɗin ya kasance ma’aikacin gwamnati wanda bai kai ƙasa da matakin aiki na GL 15 ba, yayin da ɗayan kuma dole ne ya kasance sanannen sarki ko shugaban gargajiya.

Bugu da ƙari, an hana El-Rufai yin duk wata magana a bainar jama’a dangane da shari’ar, sannan dole ne ya halarci dukkan zaman kotu.

Lauyan tsohon gwamnan, Ubong Akpan, ya ƙi yin tsokaci lokacin da ’yan jarida suka tuntuɓe shi bayan kammala zaman kotun.

Sai dai ɗan El-Rufai, wato Bello El-Rufai, ya tabbatar da cewa an bai wa mahaifin nasa beli.

Haka kuma, wani jigo na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Hayatudeen Maƙarfi, ya tabbatar da wannan lamarin, yana mai cewa belin ya zo tare da sharuɗɗa masu yawa, ciki har da buƙatun kuɗi, kadarorin ƙasa, da kuma shigar da wani sanannen basarake a matsayin mai tsaya masa.

Ya jaddada cewa dole ne a cika dukkan sharuɗɗan kafin tsohon gwamnan ya samu ’yanci, ya ƙara da cewa El-Rufai zai ci gaba da kasancewa a hannun ICPC har sai an cika sharuɗɗan.

Shi dai El-Rufa’i, ana tuhumar sa ne da laifukan almundahana na kuɗi, ciki har da zargin saka kuɗi a asusun ajiyar sa na ƙasar waje da kuma yadda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gudanar da bincike kan kuɗaɗen shigar sa.

Sai dai kuma, an dakatar da yanke hukunci kan neman belin sa a Babbar Kotun Jihar Kaduna, domin alƙalin kotun, Mai Shari’a Darius Khobo, ya ɗage yanke hukunci kan belin zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026.

An gurfanar da tsohon gwamnan a gaban babbar kotun jihar ne kan tuhume-tuhume da dama da suka shafi zargin damfara da kuma cin zarafin muƙami da ICPC ta ɗora masa.

Hukumar ICPC ta gurfanar da shi a ranar 18 ga Maris, 2026, tare da Manajan Darakta na kamfanin TMDK Terminal Limited, Amadu Sule, a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna, ƙarƙashin lamba ta ƙara KDH/KAD/ICPC/01/26.

Tuhume-tuhumen da aka fara gabatarwa sun haɗa da zargin cin amanar muƙami, damfara, yunƙurin aikata damfara, da kuma ba da wata fa’ida ta musamman ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai a ranar Litinin, masu gabatar da ƙara sun gyara tuhume-tuhumen, inda suka cire Sule daga cikin shari’ar, suka taƙaita shari’ar ga El-Rufai shi kaɗai.

An kai El-Rufa’i gaban kotun jihar ne a ranar Litinin, 13 ga Afrilu, 2026, ta hannun jami’an ICPC da na DSS. Yana fuskantar tuhume-tuhume guda tara bayan an yi gyara a ƙarar da masu gabatar da ƙara suka shigar.

Dangane da takardun kotun Jihar Kaduna, ɗaya daga cikin manyan zarge-zargen shi ne cewa tsohon gwamnan ya amince da fitar da kimanin naira biliyan 11 daga kuɗaɗen Jihar Kaduna zuwa wata ƙungiya da ba a yi mata rajista ba domin wani aikin ƙaramin layin jirgin ƙasa wanda bai kammala ba.

Haka kuma, masu gabatar da ƙara sun zarge shi da amincewa da karɓar naira miliyan 289.8 a matsayin alawus na barin aiki, adadin da aka ce ya zarce ƙa’ida, inda aka ƙayyade kusan naira miliyan 20 ne kawai, wanda hakan ya ba shi wata fa’ida ta kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

A wata tuhumar, ana zargin sa da karkatar da sama da dala miliyan 1.08 daga cikin rancen da Bankin Duniya ya bai wa Jihar Kaduna, wanda hakan ya saɓa da sharuɗɗan amfani da rancen.
Sai dai El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen.

A zaman kotu na ranar Litinin, lauyoyi masu kare shi, ƙarƙashin jagorancin Barista Ubong Akpan, sun nuna damuwa kan jinkirin da aka yi wajen ba su sababbin tuhume-tuhumen, suna mai cewa an ba su su ne a cikin kotu kawai.

Wannan ya sa alƙalin kotun, Mai Shari’a Darius Khobo, ya ɗage shari’ar domin bai wa ɓangaren kariya isasshen lokaci domin su nazarci sababbin takardun.

Tags: cin hanci da rashawaICPCKadunakotuMai Shari'a Darius KhoboMai Shari'a Rilwan AikawaNasirElrufaizargi
Previous Post

Binciken CBN: Matsalar wutar lantarki da rashin tsaro ne suka fi damun harkokin kasuwanci cikin Maris

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da tsarin da zai kawo ƙarshen ninninka kwangila, ɓarnar kuɗi da tabbatar da Ingancin ayyuka

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da tsarin da zai kawo ƙarshen ninninka kwangila, ɓarnar kuɗi da tabbatar da Ingancin ayyuka

Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da tsarin da zai kawo ƙarshen ninninka kwangila, ɓarnar kuɗi da tabbatar da Ingancin ayyuka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!