• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Binciken CBN: Matsalar wutar lantarki da rashin tsaro ne suka fi damun harkokin kasuwanci cikin Maris

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 15, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Binciken CBN: Matsalar wutar lantarki da rashin tsaro ne suka fi damun harkokin kasuwanci cikin Maris
Babban Bankin Nijeriya

Babban Bankin Nijeriya

Wani rahoto da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar a yau Alhamis, ya ce kamfanoni a faɗin Nijeriya sun bayyana cewa ƙarancin wutar lantarki da rashin tsaro su ne manyan ƙalubalen da ke addabar harkokin su a cikin watan Maris 2026, duk da cewa har yanzu suna da kyakkyawar fata game da tattalin arzikin ƙasar nan.

Rahoton ya ce: “Kashi 74.5 na masu amsa tambayoyin sun bayyana ƙarancin wutar lantarki ce babbar matsala, yayin da kashi 70.9 suka danganta rashin tsaeo, sai haraji mai yawa ko ninki-ninki ya samu kashi 69.2 na laifin matsalolin da suka addabi harkokin kasuwanci.

“Sannan kashi 66.6 na ganin ladar biyan kuɗaɗen da aka ranta a banki, wato ‘interest’ da matsalolin kuɗi ita ma matsala ce mai zaman kan ta.

“Sai kuma kashi 64.3 a matsayin manyan ƙalubale biyar da ke fuskantar kasuwanci a watan Maris 2026, suna nuna abubuwan da ke shafar daidaito da riba na ayyukan kasuwanci.”

An gudanar da binciken tsakanin ranakun 9 zuwa 13 ga Maris 2026, inda aka tattara bayanai daga kamfanoni 1,900 a fannoni daban-daban kamar masana’antu, ayyuka da noma, tare da samun kaso 99.7% na masu amsawa tambayoyin.

Duk da waɗannan ƙalubale, kamfanoni sun ci gaba da nuna kyakkyawan fata game da tattalin arzikin ƙasa.

CBN ya bayyana cewa ma’aunin amincewa ya tsaya a maki 15.6 a watan Maris, wanda ke nuna kyakkyawan fata, duk da cewa ya ragu kaɗan idan aka kwatanta da watan da ya gabata na Fabrairu.

Ana sa ran wannan fata zai ƙaru zuwa maki 43.9 cikin watanni shida masu zuwa.

A binciken fannoni daban-daban, dukkan sassa sun nuna amincewa da yanayin tattalin arziki, inda fannin noma ya fi kowa nuna kyakkyawan fata a wannan watan. Haka nan, ana sa ran dukkan fannoni za su ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba a nan gaba da kuma nan ba da daɗewa ba.

Dangane da yankuna, binciken ya nuna cewa yankin Arewa maso Gabas ne ya fi nuna kyakkyawan fata da maki 39.4, yayin da Kudu maso Gabas ya nuna rashin kyakkyawan fata da maki –5.5.

Sai dai, ana sa ran dukkan yankuna za su samu ingantuwar yanayi a watanni masu zuwa.

Rahoton ya kuma nuna cewa kamfanoni na sa ran ƙaruwa a ayyukan kasuwanci. Masu amsa tambayoyin sun nuna kyakkyawan fata game da yawan oda, ayyukan kasuwanci, yanayin kuɗin su, da samun bashi, tare da hasashen samun ƙarin ci gaba cikin watanni shida masu zuwa.

A ɗaukar ma’aikata da faɗaɗa kasuwanci, kamfanoni sun nuna shirin ƙara ɗaukar ma’aikata a watan Afrilu 2026 sakamakon hasashen faɗaɗa ayyuka. Fannin ma’adinai da haƙar duwatsu ya fi nuna ƙarfi wajen ɗaukar ma’aikata, yayin da noma ya fi nuna shirin faɗaɗa kasuwanci.

Duk da haka, CBN ya jaddada cewa ƙalubalen tsarin tattalin arziki na ci gaba da yin tasiri ga ayyukan kasuwanci. Baya ga matsalar wutar lantarki da rashin tsaro, kamfanoni sun kuma ambaci tsadar cajin bankuna, sai kuma tsauraran dokokin tattalin arziki da rashin tabbas a harkokin siyasa a matsayin ƙarin manyan ƙalubale.

CBN ya ce sakamakon binciken ya nuna buƙatar gyare-gyare a fannoni masu muhimmanci.

Rahoton ya bayyana cewa ra’ayoyin da aka tattara na kamfanoni ne kawai, kuma ba lallai ne su yi daidai da matsayar CBN ba.

Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta gyara tuhume-tuhume kan Malami, ta cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

Next Post

Kotu ta bayar da belin N200m ga Nasir El-Rufai, amma za a ci gaba da tsare shi har sai …

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Kotu ta bayar da belin N200m ga Nasir El-Rufai, amma za a ci gaba da tsare shi har sai …

Kotu ta bayar da belin N200m ga Nasir El-Rufai, amma za a ci gaba da tsare shi har sai ...

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!