Gwamnatin Tarayya ta bayyana ƙulla wata sabuwar yarjejeniya mai tsanani da hukumomin raya yankuna na ƙasar nan, inda aka gindaya masu sharuɗɗan aiki domin kawo ƙarshen ɓarna, ninninka ayyuka, da kuma tabbatar da cewa kowane kwabo na talaka ya yi amfani.
Ministan Raya Yankuna, Abubakar Momoh, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron ƙara wa juna sani na kwana uku da aka gudanar a birnin Benin na Jihar Edo.
Ministan ya nanata cewa lokacin da hukumomi ke barin ayyuka rabi da rabi ya ƙare.
A cewar sa, ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta ita ce gasar nuna iko tsakanin hukumomi da kuma yin ayyuka iri ɗaya a wuri guda, wanda hakan ke haifar da asarar kuɗaɗen ƙasa.
Ya ce: “Wannan taron ba taron shan shayi ba ne; wani mataki ne na tabbatar da cewa mun mayar da yankunan mu wuraren arziki da zaman lafiya. Daga yanzu, shugabannin waɗannan hukumomi za su sanya hannu kan takardar yarjejeniyar aiki (Performance Bond) don tantance ƙoƙarin su.”
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta sake bayar da damar fara sababbin ayyuka ba har sai an kammala tsofaffin da ke ƙasa, kuma an tabbatar da cewa mutane sun amfana da su.
Ya bayyana cewa kafa hukumomin raya yankuna a ɗaukacin shiyyoyi shida na ƙasar nan yana ƙunshe ne cikin tsarin ‘Sabunta Fata’ (Renewed Hope Agenda) na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin tabbatar da cewa babu yankin da aka bari a baya.
A nasa jawabin, Ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Uba Ahmadu, ya bayyana taron a matsayin “kira na gaggawa” ga ɗaukacin mahukunta.
Ya buƙaci hukumomin da su fito su faɗi gaskiyar matsalolin da ke damun su domin a nemo bakin zaren.
Shi ma Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Raya Yankuna, Sanata Jide Ipinsagba, ya ba da tabbacin cewa majalisa za ta sanya ido sosai kan yadda ake gudanar da waɗannan sababbin tsare-tsare.
Taron ya samu halartar wakilin Gwamna Monday Okpebholo na Jihar Edo (Mataimakin sa, Dennis Idahosa), shugabannin hukumomin raya yankuna na Arewa-maso-gabas, Arewa-maso-yamma, Arewa-ta-tsakiya, Kudu-maso-abas, Kudu-maso-yamma, da Kudu-maso-kudu (NDDC), da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa irin su UNICEF da UNDP.
Wannan sabon mataki yana nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗaura ɗamara wajen ganin an samu daidaito a fannin ababen more rayuwa, tsaro, da kuma tallafa wa matasa a ɗaukacin faɗin Nijeriya.







