Gwamnatin Tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ta shigar kan Alhaji Abubakar Malami, tsohon Antoni-Janar na Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a a zamanin mulkin Buhari, da matar sa, da ɗan sa Abdul’aziz, inda ta cire zargin da ya shafi ɗaukar nauyin ta’addanci.
A zaman kotu na yau Laraba, Akinlolu Kehinde, lauya ga Hukumar Tsaro ta DSS, ya sanar da kotu game da gyaran tuhume-tuhumen tare da neman a maye gurbin tsofaffin tuhume-tuhumen.
Sabuwar tuhumar da aka gyara ta shafi mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Shaibu Aruwa, lauyan waɗanda ake ƙara, ya tabbatar da cewa an bai wa abokan huldar sa sabuwar tuhumar, kuma ya amince a karanta masu sababbin tuhume-tuhumen a gaban kotu.
Saboda haka, an karanta masu sababbin tuhume-tuhumen, inda suka musanta laifin baki ɗaya.
Mai Shari’a mai jagorantar shari’ar, Joyce Abdulmalik, ta amince da ci gaba da sakin waɗanda ake tuhuma bisa sharuɗɗan beli da aka ba su a ranar 27 ga Fabrairu.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga Mayu da kuma 15 ga Yuni domin ci gaba da sauraren ƙarar.
A cikin sababbin tuhume-tuhumen, masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa an samu makamai da harsasai masu rai a gidan Malami da ke Birnin Kebbi.
BAYANI NA FARKO
Malami da Abdul’aziz sun fara bayyana a kotu ne a ranar 3 ga Fabrairu bayan DSS ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
DSS ta zargi Malami da ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci duk da cewa an aika masa da fayilolin shari’o’in domin gurfanar da su.
A ranar 27 ga Fabrairu, an ba tsohon AGF da ɗan sa beli na naira miliyan 200 kowannen su, tare da gabatar da mutane biyu a matsayin masu tsaya masu.







