Gwamnatin Tarayya ta samu sabon alƙawarin zuba jari na dala biliyan 1 a fannin ƙarafa, a ƙoƙarin gaggauta bunƙasa masana’antu, inda jimillar jarin kai-tsaye daga ƙasashen waje a wannan ɓangare ta haura dala biliyan 2.2 a ƙarƙashin ajandar gyaran tattalin arziki ta Bola Ahmed Tinubu.
An ƙulla sabuwar yarjejeniyar ne a ranar Talata a birnin Kolkata na ƙasar Indiya, inda Ministan Haɓaka Ƙarafa, Prince Shu’aibu Abubakar Audu, ya rattaba hannu kan wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da kamfanin Rashmi Metaliks Group kan zuba jari da ake hasashen darajar ta ta kai dala biliyan 1 cikin shekaru uku.
Yarjejeniyar ta biyo bayan rangadin masana’antar ƙarafa ta kamfanin, inda tawagar Nijeriya ta duba yadda ake gudanar da ayyuka daga sarrafa ƙarfen DRI (Direct Reduced Iron), pig iron, billets, zuwa ƙera bututun ƙarfe mai ƙarfi.
A wata sanarwa da shugabar sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta ma’aikatar, Salamatu Jibaniya, ta fitar, ta tabbatar da wannan cigaba da aka samu, tana mai bayyana shi a matsayin muhimmin mataki wajen faɗaɗa masana’antu a Nijeriya.
Sanarwar ta ce Ministan ya yaba da girman ayyukan kamfanin da kuma amfani da fasahar zamani, yana mai cewa tsarin haɗa dukkan matakai na samar da ƙarafa na kamfanin na nuna inganci da ƙwarewa wajen samar da ƙarafa na zamani.
Da yake magana bayan rattaba hannun, Audu ya ce yarjejeniyar tana nuna yadda ƙasashen duniya suke ƙara amincewa da gyare-gyaren tattalin arzikin Nijeriya da kuma damar da take da su a ɓangaren masana’antu.

Ya ce, “Yarjejeniyar da aka ƙulla da kamfanin Rashmi Metaliks Group wata babbar nasara ce a ƙoƙarin sake farfaɗo da ɓangaren ƙarafa a Nijeriya, tare da tabbatar da ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da ayyukan yi da rage dogaro da shigo da kaya daga waje.”
Audu ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwa wani ɓangare ne na dabarar jawo jarin da ke dogaro da fasaha zuwa cikin masana’antu a Nijeriya.
Ya bayyana cewa Nijeriya tana ƙoƙarin sauya matsayin ta daga mai fitar da albarkatun ƙasa kawai zuwa tattalin arziki mai ƙara darajar kayayyaki, bisa dogaro da ɗimbin arzikin ma’adinai da take da su.
Ya ce Nijeriya tana da sama da tan biliyan uku na ma’adinan ƙarfe, wasu ma suna ɗauke da kashi 67 cikin 100 na sinadarin ƙarfe, yana mai cewa bai kamata ƙasar ta ci gaba da dogaro da shigo da ƙarafa daga waje ba.
Ministan ya bayyana cewa ana kashe kusan dala biliyan 10 duk shekara wajen amfani da ƙarafa a cikin gida, yana mai cewa wannan babban giɓi ne da dole ne samar da ƙarafa a cikin gida ya cike.
Ya kuma bayyana burin Nijeriya na samar da tan miliyan 10 na ƙarafa duk shekara nan da shekarar 2030, domin mayar da ƙasar cibiyar ƙarafa a Afrika.
Yarjejeniyar da aka ƙulla da Rashmi Metaliks Group ta ƙara shiga jerin jarin da ke shigowa ɓangaren ƙarafa a Nijeriya, ciki har da wata masana’anta ta dala miliyan 400 a Jihar Ogun, da kuma wani haɗin gwiwar kamfani na Afrika da darajar sa ta kai dala miliyan 300 a Jihar Kaduna.
Haka kuma, ana samar da ayyukan tallafin makamashi, ciki har da wani shirin iskar gas na dala miliyan 500 a Ajaokuta, Jihar Kogi, domin inganta samar da gas ga masana’antu.
Audu ya ce gwamnati tana gina tsarin da zai haɗa ɓangarorin ƙarafa, makamashi, ma’adinai, sufuri da masana’antu, yana mai jaddada cewa ɓangaren ƙarafa ba zai iya bunƙasa shi kaɗai ba sai da cikakken tsarin masana’antu.
Ya kuma gayyaci masu zuba jari daga Indiya da su zo su binciki damar da ke akwai a Nijeriya, yana mai tabbatar musu da kwanciyar hankali da goyon bayan gwamnati.
A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban kamfanin Rashmi Metaliks Group, Sunil Kumar Patwari, ya ce kamfanin yana da yaƙinin wannan haɗin gwiwa kuma zai cika alƙawurran da ke cikin yarjejeniyar.
Tawagar ministan ta haɗa da manyan jami’an ma’aikatar da kuma wakilan ofishin jakadancin Nijeriya a New Delhi, ƙarƙashin jagorancin jakadan riƙo, Ubong Akpan Johnny.
Ana kuma sa ran ministan zai gana da Ministan Ƙarafa na Indiya, Shri H.D. Kumaraswamy, domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen biyu kafin dawowar sa Nijeriya.






