Gwamnatin fallasa sunayen waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya – Ga sunayen
Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin sunayen mutane da ƙungiyoyi 48 da ake zargi da alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya, a wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi na tarwatsa hanyoyin kuɗaɗen da ke tallafa wa rashin tsaro a faɗin ƙasar.
An fitar da jerin sunayen ne a ranar Asabar, 11 ga Afrilu, 2026, ta hannun Kwamitin Takunkumi na Nijeriya (NiGSAC), kuma an ɗora shi a shafin yanar gizon kwamitin, wato nigsac.gov.ng.
Jerin ya ƙunshi sunayen mutane da ƙungiyoyi da ake zargi da hannu a harkokin ta’addanci, ciki har da alaƙa da haramtattun ƙungiyoyi kamar Indigenous People of Biafra (IPOB), Ansarul Sudan, da Islamic State West Africa Province (ISWAP).
Daga cikin waɗanda aka lissafa akwai Simon Ekpa, wani ɗan Nijeriya mai ra’ayin ballewa da ke zaune a ƙasar Finland, wanda ake danganta shi da wani ɓangare na IPOB. A ranar 1 ga Satumba, 2025, wata kotu a Finland ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru shida bisa laifukan da suka shafi ta’addanci, ciki har da tunzura jama’a da kuma shiga ayyukan ƙungiyar ta’addanci.
Haka kuma an ambaci ɗan jarida kuma mawallafi daga Kaduna, Tukur Mamu, wanda a halin yanzu yake fuskantar shari’a a Nijeriya kan zargin hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci. An kama Mamu a shekarar 2022, kuma yana fuskantar tuhume-tuhume da dama daga Gwamnatin Tarayya, da suka shafi bayar da tallafin kuɗi da kayan aiki ga ƙungiyoyin ta’addanci. Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen.
Sauran mutanen da aka lissafa sun haɗa da: Abdulsamat Ohida, Mohammed Sani, Abdurrahaman Abdurrahaman, Fatima Ishaq, Yusuf Ghazali, Abubakar Muhammad, Sallamudeen Hassan, Adamu Ishak, Hassana Isah, Abdulkareem Musa, Umar Abdullahi, Bashir Yusuf, Ibrahim Alhassan, Salihu Adamu, Surajo Mohammad, Fannami Bukar, Muhammed Musa, Sahabi Ismail, Mohammed Buba, Adamu Hassan, Hassan Mohammed, Usman Abubakar, Kubara Salawu, da Rabiu Suleiman.
Jerin ya kuma ƙunshi wasu mutane kamar Simon Njoku, Godstime Iyare, Francis Mmadubuchi, John Onwumere, Chikwuka Eze, Edwin Chukwuedo, Chiwendu Owoh, Ginika Orji, Awo Uchechukwu, Mercy Ali, Ohagwu Juliana, Eze Okpoto, Nwaobi Chimezie, da Ogumu Kewe.
Ƙungiyoyin da aka ambata a cikin jerin sun haɗa da: Jama’atu Wal-Jihad, Ansarul Sudan (Ansaru), Islamic State West Africa Province (ISWAP), Indigenous People of Biafra (IPOB), Yan Group, da Yan Group NLBDG.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke gudanar da babbar shari’ar masu laifin ta’addanci, wanda ke nuna ƙarin tsaurara mataki kan waɗanda ake zargi da taimakawa ayyukan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Shari’ar, wadda aka fara a ranar Talata a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta ga an gurfanar da mutane 227 a gaban alƙalai 10. An tsaurara matakan tsaro yayin shari’ar, inda aka kawo waɗanda ake tuhuma cikin ayarin motoci masu tsaro ƙarƙashin kulawar jami’an soja, ‘yan sanda, da jami’an leƙen asiri.
Ya zuwa yanzu, an yankewa mutum biyar hukuncin ɗaurin shekaru tsakanin bakwai zuwa 20 bayan sun amsa laifuffuka da suka haɗa da sayar da dabbobi, samar da abinci, da bayar da bayanai ga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi, ya ce girman shari’ar na nuna ƙudurin gwamnati na magance ɗaukar nauyin ta’addanci tare da tabbatar da an yi adalci.
Ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta jajirce wajen tabbatar da bin doka da oda yayin gurfanar da masu hannu a ta’addanci gaban kuliya.”
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka fito daga shari’ar shi ne hukuncin da aka yanke wa Babagana Habeeb, tsohon ɗan takarar majalisar dattawa a Jihar Borno, na ɗaurin shekaru 10 saboda sayar da man fetur ga ‘yan ta’addan Boko Haram.
An yanke masa hukunci ne bayan ya amsa laifi kan tuhume guda ɗaya na taimakawa ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansa.
Ya amince da cewa ya rika samar da man fetur ga ‘yan tada kayar baya a Arewa maso Gabas, duk da cewa ya ce ma’aikatan gidan mai nasa na iya kasancewa ne suka gudanar da wasu daga cikin mu’amalolin.
A yayin shari’ar, Habeeb ya roƙi sassauci, yana mai cewa ya shafe sama da shekaru 10 a tsare ba tare da hulɗa da iyalansa ba, kuma yana da mata biyu da ‘ya’ya shida.
Lauyan Gwamnatin Tarayya, David Kaswe, ya ƙi amincewa da roƙon, yana mai cewa ayyukan wanda ake tuhuma sun taimaka wajen jawo mutuwar mutane da raba jama’a da muhallansu. Ya buƙaci kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 20.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Peter Lifu ya bayyana cewa babu hujjar da ta nuna Habeeb mamba ne na wata ƙungiyar ta’addanci ko ya samu horon makamai, yana mai cewa tuhume-tuhumen sun ta’allaka ne kawai kan sayar da mai ga ‘yan ta’adda.
Ya kuma lura cewa ɓangaren masu gabatar da ƙara bai musanta cewa Habeeb ya shafe sama da shekaru 10 a tsare ba. Daga nan sai ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10, tare da umartar cewa hukuncin ya fara aiki daga ranar da aka kama shi.
Kotun ta kuma bayar da umarnin a sake shi bayan ya kammala zaman hukuncinsa, tare da shawarar a yi masa gyaran hali.
Ga cikakken jerin sunayen da aka sabunta a ranar Asabar:
Abdulsamat Ohida
Mohammed Sani
Abdurrahaman Abdurrahaman
Fatima Ishaq
Tukur Mamu
Yusuf Ghazali
Muhammad Sani
Abubakar Muhammad
Sallamudeen Hassan
Adamu Ishak
Hassana Isah
Abdulkareem Musa
Umar Abdullahi
Abdurrahaman Ado
Bashir Yusuf
Ibrahim Alhassan
Muhammad Isah
Salihu Adamu
Surajo Mohammad
Fannami Bukar
Muhammed Musa
Sahabi Ismail
Mohammed Buba
Jama’atu Wal-Jihad
Ansarul Sudan (Ansaru)
Islamic State West Africa Province (ISWAP)
Indigenous People of Biafra (IPOB)
Yan Group
Yan Group NLBDG
Adamu Hassan
Hassan Mohammed
Usman Abubakar
Kubara Salawu
Rabiu Suleiman
Simon Njoku
Godstime Iyare
Francis Mmadubuchi
John Onwumere
Chikwuka Eze
Edwin Chukwuedo
Chiwendu Owoh
Ginika Orji
Awo Uchechukwu
Mercy Ali
Ohagwu Juliana
Eze Okpoto
Nwaobi Chimezie
Ogumu





