• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Mahanga

Rayuwa: Kaɗan Daga Cikin Labarin Halin Rayuwar Da Nake Ciki Da Kuma Matsaya Ta A Siyasar 2027 – Umar Tata

Umar Abdullahi Tsauri Tata by Umar Abdullahi Tsauri Tata
April 10, 2026
in Mahanga
A A
0
Rayuwa: Kaɗan Daga Cikin Labarin Halin Rayuwar Da Nake Ciki Da Kuma Matsaya Ta A Siyasar 2027 – Umar Tata
Alhaji Umar Abdullahi Tsauri (Tata)

Alhaji Umar Abdullahi Tsauri (Tata)

Lokacin da ta kira ni, ban daɗe daga tashi daga barci ba. Ƙanwa ta ce ta ɓangaren mahaifiya ta. Mukan jima ba mu gaisa ba, amman tana da ƙoƙarin ganin cewa zumuncin da ke a tsakanin mu bai yi rauni ba. Na amsa wayar na ce, “Amina kina lafiya?” Ta ce, “Lafiya lau.” “Yaya gidan, ya iyali?” “Duka alhamdu lillahi.” Babu abin da ya fito bakin ta sai take ce mani, “Ni dai wallahi sau biyu ina mafarkin ka kuma ba ni jin daɗin yanda nike ganin ka a cikin mafarki.”

Duk rai yana son ya ji magana mai daɗi ko da kuwa ƙarya ce. Magana irin wannan tana da sosa rai. Na ce, “Amina yaya kike gani na a cikin mafarki?”

Ta ce, “Wallahi sau biyu ina ganin ka kwance kana barci, ka lulluɓe da tsumman bargo, ga wasu bayin Allah nan cikin fararen kaya suna son su iso wajen ka amman abin ya gagara.” Ta ce ita kuma a ɗan sanin da ta yi, tsumman bargo alama ce ta talauci. Subhanallahi!

Bacin ta gama, ni kuma na tabbatar mata cewa talauci kam ina fama da shi sai dai abin da Allah ya yi daga cikin rahamar shi. A lokacin, gidaje biyun da nike zaune ni da iyali na duk na haya ne kuma hayar ta ƙare, masu gidajen sun azabtar da ni in tashi in ba su gidajen su tunda na kasa sabunta hayar. Babu kuɗin da zan biya kuma babu inda zan samo su. Ɗaya daga cikin su ma har ya kai ni kotu kuma kotu ta ba ni wa’adin tashi. Wannan duk ya biyo bayan asarar duk wani gida nawa da na mallaka a rayuwa, in ban da guda ɗaya dake a Dutsin-ma, wanda shi ma a cikin garari yake a lokacin. Ba ni da kuɗin biyan hayar kuma ba ni da inda za ni je a biya mani. Wata sa’a in yi kuka ni kaɗai cikin duhu ba tare da iyali sun sani ba, saboda na san irin cin mutunci da wulaƙancin da ake fuskanta in kotu za ta fitar da kai daga cikin gida; na ga wannan wulaƙanci a kan gidaje na biyu da na yi asarar su, kuma ina tausaya ma iyali na da ƙara fuskantar irin wannan tozarcin da wulaƙancin. Wata sa’a kuma ni kaɗai sai in taushi kai na in ba kai na ƙwarin gwiwa cewar duk mai bayarwa, sai dai jarabawa, amman Allah ba zai taɓa hana shi ba. Masallaci a lokacin sai ya zamo wurin da na fi sha’awar zama a rayuwa ta.

Amina ta ce, bayan tabbatar mata da na yi na halin rashin da nike ciki ba tare da ba ta wani labari ba, tunda ba ni zaton tana da taimakon da za ta iya yi mani, da za ni amince da ta haɗa ni da wani mutum wataƙila, cikin yardar Ubangiji, a sami taimako ta wajen shi. Irin waɗannan maganganun an yi mani su a rayuwa babu adadi, amman ba ni yarda da su saboda na san komai rubutacce ne daga Allah kuma ɗan’adam ba ya da abin da za ya iya yi mani saɓanin abin da Allah ya ƙaddara mani. Amman a wannan ranar, cikin taimakon Allah, a karo na farko, sai na amince mata da ta haɗa ni da mutumen. Dalili kuwa ina son kauce ma masu zargi da zagi na da cewa ni ba ni ɗaukar shawara duk da ba ni da tunanin wani alkhairi a cikin abin. In har sihiri ne, kamar yanda wasu suka sha faɗi, particularly masu raunin imanin, cewa wannan abin ba na Allah da Annabi ba ne, to na rufe bakin su. Babu sauran zargi a tsakani. Bugu da ƙari sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiya ne, kuma ni ba kowa ba ne, don fiyayyen halitta ma, Annabi Muhammad SAW, an yi mashi kuma ya kama shi, to ballantana ni? In kuma ba shi ba ne ba, to addu’a abin so ce daga kowane irin ɗan’adam saboda ban san irin baki da darajar da Allah ya yi mashi ba. A sanadiyyar haka ne na shiga wata sabuwar rayuwa da malamin da Amina ta haɗa ni da shi. Mutum ne kamili, mai ilimi na addini da zamani, mai tsoron Allah kuma mai tsaya ma gaskiya.

Watau wanda duk ya ce maka babu sihiri ko tsafi, to kawai bai taɓa zama victim na matsafan ba ne, ko kuma ko da ya zamo to Allah bai haska mashi shi ba ne ballantana ya gane. Sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiya ne. Ni Tata victim ne nasu daga ɗan abin da Allah Ya bayyana mani a kan kai na. A kai na an bizne baƙin doki da rai a tsohuwar maƙabarta ta Unguwar Kudu a Dutsin-ma. A kai na an kashe makaho an bai wa macijiya shi ta haɗe shi da layu duk don kada in sami biyan bukata a rayuwa. A kai na an fitar da sabuwar gawa daga cikin kabari an cire mata kwanya an cika ta da layu an maida ta an bizne don in haukace. Ban da baƙaƙen shanu, jakuna, macizai da karnuka ba iyaka da aka yi amfani da su. Duk wannan an yi ne kawai don in yi asarar damar da nike da ita ta taimakon al’umma da addinin Allah da kuma tsoron kada in yi gwamnan Katsina.

Kafin 2011 ni ba ɗan siyasa ba ne. Ni ma’aikacin gwamnati ne kuma babu abin da nike ji ma daɗi, nike so, irin aiki na. Kishin ƙaramar hukuma ta ta Dutsin-ma da son nuna godiya ga gwamnan da ke ci a lokacin, Ibrahim Shehu Shema, a kan ayyukan cigaba da na ga ya yi a jihar, ya sanya na shigo siyasa domin in kama mashi ya ci second term. Ba don komai ba sai don faɗar Allah cewa babu sakamako ga aiki kyakkyawa face alkhairi. Saman wannan, ina kuma da kwaɗayin in ya samu nasarar second term, to ya zamanto encouraged by nasarar da ya samu ya ƙara lunka alkhairi a jihar saman abin da ya yi. Bacin wannan, ba ni da wani dalilin da ya sa na shigo siyasa. Amman Allah da ke tsara rayuwa yanda ya so, sai ga shi wannan gudunmuwa da na shigo in bada, ta jawo mani zama a cikin siyasa har da takara ta gwamna, abin da ba ni sha’awa a lokacin kuma ban taɓa tunanin ta ba, wanda ta ja har ta kai na rabu da aikin nan wanda na fi so saman komai.

Abin da duk ya faru ya faru a 2015 wanda tun daga lokacin ne rayuwa ta ta canza. Na yi ƙoƙarin komawa bakin aiki na amman sau goma sha biyu ina rubuta takardar janye takardar retirement ɗina amman duk lokacin da aka fara aiki a kan takardar tawa sai file ɗin nan ya ɓace, ko sama ko ƙasa ba za a ƙara ganin shi ba. Cikin wannan lokacin ne na rasa gidaje na na koma haya. Na rasa motoci na na koma tafiya ƙasa. Na rasa masoya na na wannan lokacin sai dai wasu, waɗanda su ban ma amfane su ba a lokacin da nike da shi ba, saboda ban san su ba, su ne suka tsaya mani. Na rasa duk wani mai taimako wanda zai iya tausaya mani in sami abin yi don tsare mutunci na. Harka ko ya take in na ɗauko ta sai an zo kusan 99% na nasara sai ta rushe a koma square one kamar ba a taɓa yi ba!

A cikin wannan halin ne Allah ya sa Amina ta kira ni, lokacin da sutura ta sawa ma tana neman ta gagare ni. Babbar godiya ta ga Allah ita ce a wannan lokacin ne Allah ya ɗauki rayuwar mahaifiya ta, ba ta ga irin wulaƙanci da jarabawar rayuwar da na shiga ba. Ta bar duniya da tunanin ɗan ta jarumi ne kuma mai arziki!

Taimakon Allah na zuwa daga inda rai bai taɓa zuwa ba, haka ma zuciya ba ta taɓa tunani ba. Abubuwa da yawa sun faru, kuma Allah ya bayyanar da abin da ya so daga cikin ikon Shi. Na ga abin mamaki na ga abin tsoro. A sanadiyyar haka na san ko wanene Allah. Wanda duk ya gaya maka ya san Allah to ya bari har Ya taɓa shi sannan zai san ko waye Allah. Amina da Malam, Allah ya saka maku da alkhairi.

Malam ya wahala a ƙoƙarin taimaka mani. Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, Allah ke kuɓutar da Malam a kan ido na. Ya yi asarar lafiya a kan ido na, ya yi asarar dukiya a kan ido na, ya yi asarar abokanan hulɗar shi a kan ido na, sannan a kan ido na za a halba Malam ya bugo ceiling kafin ya dawo ƙasa ya yi jina-jina sannan ga wasu manyan lizards da ban taɓa ganin irin su ba sun kama wuyan shi yana makyarkyatar mutuwa. Na ga tashin hankali. Wanda rayuwa ba ta taɓa ba zai zaci tatsunniya nike.

Sannu-sannu taimakon Allah ya zo mamu ta ɓangaren da ba mu zata ba.

Lokacin da nike hidima, kafin zaɓen 2015, ashe akwai shugaban da na yi ma laifi a Jihar Katsina. A irin nashi tunanin, wai na shigo cikin siyasar shi, ba don komai ba, sai don na yi amfani da inuwar shi in yi suna sannan in raba shi da jama’a. Saboda haka ya ɗauki mataki kai na. Matakan guda biyu ne. Mataki na zahiri da mataki na baɗini. Matakin zahiri shi ne a raba ni da aiki na, saboda ai sai ina da aiki za ni sami abin da zan ba jama’a da har suke bi na. A kan wannan an yi petitions babu iyaka zuwa wajen Head of Service of the Federation, Minister of Finance, Minister of Defence da kuma Secretary to the Government of the Federation. Wanda daga ƙarshe da ya ga bai sami nasarar da yake nema ba ya rubuta ma Shugaban Ƙasa Jonathan kuma ya ɗauka da hannun shi ya kai ma shi. Duka Allah ya kare ni, babu inda ya sami biyan buƙatar da yake so. Bacin waɗannan petitions ɗin, bai yi ƙasa a gwiwa ba sai da ya bi ni da petitions wajen jami’an tsaro: EFCC, ICPC, Code of Conduct Bureau da kuma Nigeria Police. Su ma dai Allah bai ba ni kunya ba, don Ya tsaya mani. Haka aka yi su a banza sai ɗan kamun da aka yi mani wanda na yi zaman cell na EFCC na sati 4.

Matakin baɗini kuwa shi ne aka bazu cikin malamai na tsubbu a kan yanda za a yi da ni. A nan ne aka ɗauki suna na aka kai ma wani shahararren matsafi mai bautar rana wanda ke a Indiya. Buƙatar guda 4 ce. Na farko dai a ɗauki rayuwa ta, in bar duniyar kwata-kwata. In haka bai yiwu ba, a raba ni da lafiya ta, ya kasance ina duniya amman kamar ba ni duniyar saboda ciwo ko lalacewa ta hauka ko wani abu makamancin haka. Na ukku, a raba ni da duk wani abin da ake kira wadata ko samu, in rabu da abin da ke gare ni, sannan duk wata ƙofa ko kafa ta samu a lalata ta yanda arziki sai dai in gan shi a wajen wasu, ba dai in same shi ba. Na ƙarshe shi ne a raba ni da duk wani mai so na, a saka ƙyama ta a zukatan al’umma yanda babu wanda zai iya taimako na.

Ni ba wannan ne ya ɓata mani rai ba sai kasancewar a wannan buƙatar tashi ya haɗa da children ɗina, cewa su ma yana son kar su yi albarka a rayuwa domin suna na ya ɓace a bayan ƙasa ko bayan rai na. Wannan shi ne ya fi yi mani zafi. In har ni akwai laifin da na yi mashi, in har akwai shi kenan, saboda ni taimakon shi na yi, to laifin me ɗan da na haifa ya yi mashi? Allah ya isa! Tun daga wancan lokacin har ya zuwa yau, akwai abin da yake aika ma shi wannan matsafin bayan duk kwana 75 don biya ma baƙaƙen aljannun da suka addabe ni buƙata don kar in sami sukuni ko faraga a rayuwa har in koma ga Mahalicci na.

Lokacin da suke ƙoƙarin raba ni da duk wata hanyar samun taimako ko masu taimakawa, sai Allah ya bar ni da talakawa na. A duk ranar duniya ba a rasa talaka ɗaya, namiji ko mace, da zai yi mani addu’a ta alkhairi da tausayawa, saboda talakan Jihar Katsina yana da yaƙinin cewa samu na samun shi ne. Addu’ar su da ƙaunar su ita ta kawo har Allah ya tausaya mani ya tsare mani rayuwa ta, lafiya ta da mutunci na, saɓanin abin da wannan bawa Allah ya ƙudurta a kai na. Waraka kuma ta duniya, bi’iznillahi ina da yaƙinin cewa Allah ba azzalumi ba ne kuma ba ya son zalunci, ba zai bar ni cikin wannan halin ba saboda wancan bawan nashi ya ji daɗi. Da yardar Allah wata rana sai na fita, sai an ga kamar ba a taba yi ba!

Da dama ana ta magana a kan matsaya ta a siyasa, wanda har ya sa wata sa’a ra’ayin zuciya yana neman ya rinjaye ni zuwa aikata abin da ba hali na ba. A rayuwa ba a taɓa yi mani alkhairi ban rama ba, sai dai in ba ni da hali, ballantana in maida sharri. Wannan ba hali na ba ne. Duk wanda ya san Dikko Raɗɗa, ya san shi da ba ya son abubuwa guda biyu. Na farko, Dikko ba ya son rabuwa da kuɗi ko kaɗan, sai dole. Na biyu, Dikko ba ya son a tambaye shi kuɗi, to kun kau saɓa. Allah ya sani, ina cikin mutane ‘yan kaɗan da ke karya wannan dokar ta Dikko kuma ya yi mani ko ba ya so. Dikko ya zo gida na ya bai wa iyali na N1.5m. Dikko ya biya ma yarinya ta da ke a private university school fees lokacin da ake neman a kore ta saboda na kasa biya mata don ba ni da su. Dikko ya ba ni N10m na biya muhalli ga iyali na a lokacin da dukkanin su suna gidajen iyayen su saboda ba ni iya biyan hayar. Dikko ya ba ni mota ta hawa sau biyu. In yi mashi ƙarya ya ba ni, in gaya mashi gaskiya ya ba ni, ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Dalilin hakan ne ya sa na sauko ƙasa na zo na fara yi mashi programme a gidan rediyo domin in nuna godiya ta a gare shi sannan in saka mashi kwatankwacin hali na. Saboda haka zan tsaya da Dikko, da daɗi babu daɗi, har Allah ya kai mu ga nasara ya kammala wa’adin shi na biyu, saboda shi kaɗai ne ya yi mani irin wannan taimakon duk duniya a lokacin da ba ni da kowa sai Allah.

Tabbas, a tare da shi akwai waɗanda ba su ƙauna ta, kuma in suna da iko ba za su so in samu ko pure water ba ballantana wani matsayi. Zan yi haƙuri in taimake shi daga nesa ba tare da na shige mashi ba har ni ma Allah ya kawo mani tawa mafitar. Ba za ni bar APC ba, ba za ni yi faɗa da APC ba, haka zalika ba za ni guji Dikko Raɗɗa ba. Masoya na da wannan matakin nawa bai yi ma daɗi ba ko ya ɓata masu rai ko ya yi disappointing nasu, including a part of my family, ina neman afuwar su da kuma ba su haƙuri. I would rather die poor with a clean conscience than swim in opulence with a fractured ego. In-sha Allahu ba za ni bar ma ɗiya na abin faɗi ba a rayuwa.

Na gode ƙwarai.

Tags: APCDikko Umar RaɗɗaKatsinarayuwatsafiUmar Abdullahi Tsauri (Tata)Umar Tata
Previous Post

EFCC ta kama makarantar ‘yan damfarar intanet a Abuja, ta cafke mutum 31

Next Post

Related Posts

Kumbon Voyager 1 Ya Kafa Tarihi
Mahanga

Kumbon Voyager 1 Ya Kafa Tarihi

November 19, 2026
Taron Kaduna: Arewa ta Bayyana Matsayar Ta Kan Tinubu
Mahanga

Taron Kaduna: Arewa ta Bayyana Matsayar Ta Kan Tinubu

October 25, 2026
Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’id
Mahanga

Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’id

August 23, 2026
Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa
Mahanga

Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa

July 22, 2026
Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya
Mahanga

Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya

July 21, 2026
Aikin sake gina titin Abuja–Kaduna ya kai kashi 85% na kammaluwa – Gwamnati
Mahanga

Yadda Shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ ya Sauya Zancen Ayyukan Gwamnatin Tarayya a Arewa

July 13, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!