Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci manyan jami’an tattalin arzikin Nijeriya da su gaggauta fito da matakan da za su rage wa talaka raɗaɗin da rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya ya jefa shi a ciki.
Shugaban ya bayar da umurnin ne a ranar Juma’a, yayin wata liyafa da aka shirya masa a birnin Yenagoa, bayan ya ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Douye Diri ya samar a Jihar Bayelsa.
Tinubu ya ɗora wa Ma’aikatar Kuɗaɗe da ta Tsare-tsare, tare da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, nauyin duba hanyoyin da za a sauƙaƙa wa ‘yan ƙasar nan halin matsin tattalin arziki.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya fitar daga Yenagoa, an bayyana cewa Tinubu ya amince cewa lallai rikicin duniya ya janyo tsadar rayuwa, musamman ta fuskar farashin man fetur da ke addabar jama’a.

Ya ce: “Ina jin koke-koken ku ta kowane ɓangare na tattalin arziki. Farashin mai na ratsawa, amma dole mu yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya.”
Tinubu ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin sa mai kula da jin daɗin jama’a ce, kuma za ta zauna da masana domin fito da lissafin da zai sauƙaƙa wannan nauyi da ya danne kafaɗar talaka.
Haka zalika, ya jaddada aniyar jam’iyyar APC na inganta jin daɗin jama’a ta hanyar ayyukan raya ƙasa da ke taɓa rayuwar talaka kai-tsaye.
“Mutane na buƙatar ganin an fassara mulki ta hanyar hanyoyin mota, gadoji, wutar lantarki, da samar da ayyukan yi,” inji shi.

A yayin ziyarar, Shugaban ya ƙaddamar da wasu gagaruman ayyuka a jihar, ciki har da tashar samar da wutar lantarki ta iskar gas mai ƙarfin megawat 60 a ƙauyen Elebele, da gadar Angiama zuwa Oporoma mai tsawon mita 630, da kuma wata sabuwar babbar hanyar shiga Yenagoa.
Tinubu ya yaba wa Gwamna Diri kan yadda yake tafiya tare da tsarin ‘Sabunta Fata’ na Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin jiha da tarayya shi ne sirrin kawo cigaba cikin hanzari.
Kafin kammala jawabin nasa, Shugaban ya buƙaci mahalarta taron da su yi shiru na tsawon minti guda domin karrama sojojin da suka riga mu gidan gaskiya da kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, marigayi DSP Alamieyeseigha.
A nasa jawabin, Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa goyon bayan da Gwamnatin Tarayya ta ba shi ne ya ba jihar damar kammala ayyukan wutar lantarkin, wanda hakan zai bunƙasa harkokin kasuwanci da inganta rayuwar al’ummar jihar.







