• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kafafen yaɗa labarai babban makami ne na isar da saƙo da shafar tunanin al’umma kan alƙibla – Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 24, 2026
in Labarai
A A
0
Kafafen yaɗa labarai babban makami ne na isar da saƙo da shafar tunanin al’umma kan alƙibla – Idris
Alhaji Mohammed Idris

Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce kafafen yaɗa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, ƙarfafa ɗaukar nauyin abin da ka aikata, da kuma jagorantar alƙiblar ƙasa.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a lokacin wani taron wayar da kai ga kafafen yaɗa labarai kan yaƙi da halasta kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci (AML/CFT).

Babban Sakataren Hukumar Kula da Ayyukan Jarida ta Nijeriya, Dakta Dili Ezughah, shi ne ya wakilci ministan.

A jawabin sa, Ministan ce: “Kafafen yaɗa labarai ba ‘yan kallo kawai ba ne; suna taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, ƙarfafa ɗaukar nauyin abin da mutum ya aikata da kuma tasiri a alƙiblar ƙasa. Ta hanyar sahihan rahotanni, binciken jarida mai zurfi da kuma wayar da kai, suna ƙarfafa jama’a tare da taimaka wa yaƙi da cin hanci da rashawa.”

Ministan ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ɗaukar matakai na musamman domin yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma haramtattun kuɗaɗe.

Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da aka aiwatar sun ƙarfafa tsarin tattara bayanan kuɗi, sun inganta sa ido kan hadahadar kuɗi masu alamar tambaya, tare da ƙara bin ƙa’idojin duniya.

Idris ya kuma nuna rawar da muhimman hukumomi suke takawa, ciki har da Hukumar Tattara Bayanai kan Harkokin Kuɗi ta Nijeriya, yana mai cewa ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi ya taimaka wajen ganowa da kuma daƙile laifuffukan kuɗi.

Idris ya ce: “A matakin yankuna, Nijeriya tana aiki tare da ƙasashen Yammacin Afrika wajen yaƙi da laifuffukan kuɗi da ke wuce iyakokin ƙasashe.”

Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da aka yi a ɓangaren kuɗi, tare da goyon bayan Babban Bankin Nijeriya, suna taimakawa wajen inganta gaskiya da dawo da aminci a tattalin arziki.

Ministan ya amince da ƙalubalen da kafafen yaɗa labarai suke fuskanta, ciki har da wahalar rahoton laifuffukan kuɗi, yaɗa bayanan ƙarya, ƙarancin kayan aiki da kuma matsalolin tsaro.

Ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ’yan jarida tare da bunƙasa ƙwarewar su.

Ya ce: “Yaƙi da cin hanci da rashawa nauyi ne a wuyan kowa. Gwamnati da kafafen yaɗa labarai ba za su iya yin shi su kaɗai ba. Amma idan muka haɗa kai, za mu iya gina Nijeriya inda gaskiya ta zama ruwan dare kuma cin hanci da rashawa ba su da wurin ɓoyewa.”

Tags: kafafen yaɗa labaraiMohammed Idris
Previous Post

Tinubu yana murɗe wuyan dimokiraɗiyya — Nijeriya na gangarawa zuwa mulkin kama-karya – Atiku

Next Post

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!