• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Harin Maiduguri: Tinubu ya tura manyan hafsoshi Borno don magance ta’addanci

Wakilin Mu by Wakilin Mu
March 17, 2026
in Tsaro
A A
0
Harin Maiduguri: Tinubu ya tura manyan hafsoshi Borno don magance ta’addanci
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhinin sa game da sabon harin ta’addanci da aka kai birnin Maiduguri na Jihar Borno, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin ɗacin rai da ban-takaici.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 17 ga Maris, 2026, Tinubu ya jajanta wa mutanen da suka rasa rayukan su da kuma waɗanda suka jikkata, yana mai jaddada cewa gwamnati tama tare da jama’ar Borno a wannan mawuyacin lokaci.

Shugaban ya bayyana cewa waɗannan hare-hare suna nuna alamun fargaba da matsin lamba da ’yan ta’addan ke fuskanta daga dakarun tsaron Nijeriya.

“Waɗannan ayyukan ta’addanci yunƙuri ne na ƙarshe na matsananciyar fargaba da waɗannan masu laifin suke yi domin dasa tsoro a zukatan mutane, sakamakon irin luguden wutar da suke fuskanta daga jami’an mu,” inji shi.

Tinubu ya ƙara da cewa, a taron tsaro da ya gudanar a ƙarshen makon jiya, ya amince da samar da ƙarin kayan aiki da tallafin ayyuka ga hukumomin tsaro domin ƙarfafa dabarun su na yaƙi da ta’addanci.

Domin tabbatar da an magance lamarin cikin gaggawa, Shugaban ya ba wa manyan hafsoshin tsaro na ƙasa umurnin gaggawa na su koma birnin Maiduguri domin jagorantar ayyukan tsaro da kan su.

Haka kuma, ya umurci hukumomin agajin gaggawa da su tabbatar da sun ba duk waɗanda suka jikkata kulawar da ta dace.

A ƙarshe, ya jaddada cewa babu wani lungu a Nijeriya da zai zama wurin ɓuya ga ’yan ta’adda, inda ya ce: “Ba za mu taɓa miƙa wuya ga tsoro ba. Za mu nemo su, mu fuskance su, kuma mu murƙushe su baki ɗaya.”

Tags: BornohariMaidugurita'addanciTinubutsaro
Previous Post

Maiduguri: Mutum 23 suka rasu, 146 suka jikkata, yayin da sojoji na gargaɗin akwai ‘yan harin ƙunar baƙin wake da dama a Borno

Next Post

Taron APC na ƙasa zai nuna haɗin kai da ɗa’a – Idris

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Taron APC na ƙasa zai nuna haɗin kai da ɗa’a – Idris

Taron APC na ƙasa zai nuna haɗin kai da ɗa’a – Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!