• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya nemi amincewar Majalisa kan naɗin Lamiɗo Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan CBN

Wakilin Mu by Wakilin Mu
March 11, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tinubu ya nemi amincewar Majalisa kan naɗin Lamiɗo Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan CBN
Alhaji Lamiɗo Abubakar Yuguda

Alhaji Lamiɗo Abubakar Yuguda

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Lamiɗo Abubakar Yuguda a matsayin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), sai dai naɗin zai fara ne bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi.

Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya faɗa a cikin wata sanarwa a yau Laraba cewa an yi wannan naɗi ne bisa tanadin Sashe na 8(1) na Dokar Babban Bankin Nijeriya ta shekarar 2007.

Naɗin Yuguda ya biyo bayan naɗin tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Bala Bello, a matsayin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tattalin Arziki da Siyasa.

Tinubu ya buƙaci sababbin masu riƙe da muƙaman da su gudanar da ayyukan su cikin ƙwazo, ƙwarewa da sadaukarwa domin tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Nijeriya da kuma bunƙasa shi.

Shi dai Lamiɗo Yuguda, ya taɓa riƙe muƙamin Daraktan Janar na Hukumar Kula da Kasuwar Hadahadar Kuɗi ta Nijeriya (SEC) daga 2020 zuwa 2024.

Yuguda ya kammala karatun sa a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya inda ya samu digirin BSc a fannin Akanta a 1983. Daga bisani ya samu digiri na biyu (Master’s) a fannin Money, Banking and Finance daga Jami’ar Birmingham da ke Birtaniya a 1991.

Shi memba ne na Cibiyar Ƙwararrun Akantoci ta Nijeriya (ICAN) kuma yana da shaidar ƙwararrun masu nazarin jarin kasuwa ta CFA.

Yuguda ya fara aikin sa ne a Babban Bankin Nijeriya (CBN) a cikin 1984 a matsayin Babban Mai Kulawa (Senior Supervisor) a Sashen Ayyukan Kuɗaɗen Ƙasashen Waje.

A 1997 ya shiga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) a matsayin masanin tattalin arziki a sashen Afrika, inda ya yi aiki har zuwa 2001 kafin ya koma CBN.

Ya yi ritaya daga CBN a 2016 bayan ya yi shekaru shida a matsayin Daraktan Sashen Kula da Ajiyar Kuɗaɗen Ƙasa (Reserve Management Department).

Tags: CBNLamiɗoYugudanaɗiTinubu
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ce haɗaɗɗiyar hanyar yaɗa labarai za ta ƙarfafa daidaiton tsaron ƙasa, ta yaba da gyaran iyakoki ta amfani da fasaha

Next Post

Sarki Aminu Ado Bayero ya sanar da ‘yan sanda zai yi hawan Sallah yayin da ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Sarki Aminu Ado Bayero ya sanar da ‘yan sanda zai yi hawan Sallah yayin da ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli

Sarki Aminu Ado Bayero ya sanar da ‘yan sanda zai yi hawan Sallah yayin da ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!