Rikicin Masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ya sake kunno kai inda Sarkin Kano na 15 a jerin Fulani, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya a Jihar Kano cewa yana shirin gudanar da Hawan Sallah.
Sanarwar tasa ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin tashin hankali a cikin tsohuwar masarautar, kuma kwanaki kaɗan kafin Kotun Ƙoli ta Nijeriya ta yanke hukunci mai muhimmanci kan shari’ar da ta daɗe tana gudana game da tsarin Masarautar Kano.
A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 7 ga Maris, 2026, fadar Aminu Ado Bayero ta sanar da ‘yan sanda cewa suna shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah.
Wasiƙar, wadda aka aika wa Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ta bayyana cewa za a gudanar da ayyukan Durbar ne daga fadar sarkin da ke Fadar Nasarawa a Kano.
Sakataren sarkin, Abdullahi Haruna Ƙwaru, shi ne ya sanya hannu kan wasiƙar, inda ya bayyana cewa shirin bukukuwan ya riga ya samu amincewar Sarki Aminu Ado Bayero da membobin majalisar sa.
A cewar wasiƙar, bukukuwan Sallah da aka shirya za su ƙunshi jerin gwanon dawakai da suke daga cikin manyan al’adun Kano.
Fadar ta bayyana cewa bukukuwan za su haɗa da shahararrun bukukuwan Durbar kamar: Hawan Sallah, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da Hawan Panisau.
Wannan jerin gwanon doki mai ƙayatarwa wanda ya ƙunshi raka sarki da nune-nunen al’adu da kuma tsarin sarauta, yana daga cikin manyan bukukuwan gargajiya a Arewacin Nijeriya.
Fadar ta kuma bayyana cewa cikakken jadawalin bukukuwan—wanda ya haɗa da ranaku, wurare da kuma lokutan gudanar da tarurrukan—an haɗa shi da wasiƙar sanarwar, sannan an tura shi ga hukumomin tsaro da abin ya shafa domin su shirya yadda ya kamata.
Har ila yau, fadar ta nuna godiya ga hukumomin tsaro saboda ci gaba da haɗin kai da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk faɗin Jihar Kano.
Wannan sanarwa ta zo ne bayan wasu matsalolin tsaro da suka taɓa tasowa a baya dangane da bikin hawan Sallar.
A baya dai hukumomi sun daƙile gudanar da bukukuwan Durbar ɗin bayan tashin hankali ya ɓarke sakamakon taƙaddamar da je tsakanin shi Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na 16 na Fulani, Dakta Muhammadu Sanusi II.
Rikicin da ke tsakanin sarakunan biyu ya kasance batu mai matuƙar muhimmanci a jihar, inda magoya bayan kowanne daga cikin su yake iƙirarin cewa shi ne halastaccen sarki bayan wasu sauye-sauyen siyasa da shari’a da suka shafi masarautar.
Hukumomin tsaro sun taɓa gargaɗin cewa manyan tarukan jama’a da suka shafi wannan rikici na iya haifar da tashin hankali idan ba a kula da su yadda ya kamata ba.
Wani abu da ya ƙara dagula yanayin shi ne hukuncin da ake sa ran Kotun Ƙoli ta Nijeriya za ta yanke cikin kwanaki kaɗan kan shari’ar da ta shafi Masarautar Kano.
A halin yanzu sai kotun tana nazarin ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan sauye-sauyen tsarin masarautar da gwamnatin jihar ta yi, da kuma batun mayar da wasu sarakunan gargajiya kan kujerun su da kuma amincewa da su.
Majiyoyi da ke da masaniya kan shari’ar sun shaida wa News Point Nigeria cewa hukuncin zai tantance halaccin sauya tsarin masarautar, tare da fayyace iyakar ikon gwamnatin Jihar Kano kan cibiyoyin sarauta.
Hukuncin na iya kuma warware tambayoyin da suka rage game da amincewa da iko a cikin tsarin masarautar, wanda ya kasance cibiyar rikicin siyasa da al’adu a ‘yan shekarun nan.
Tsawon ƙarnuka, bikin Durbar ba wai kawai nuni ne na al’adu ba, har ma alama ce ta ikon sarauta da haɗin kan al’umma a Kano.
Sai dai kuma, yayin da rikicin masarautar bai warware ba kuma ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli, bukukuwan Sallah na bana na iya ɗaukar ma’ana ta siyasa da alama fiye da yadda aka saba.
Duk da haka, fadar Aminu Ado Bayero ta bayyana fata cewa bukukuwan Sallah masu zuwa za su gudana cikin lumana.
Ta yi addu’ar samun natsuwa da nasarar gudanar da bukukuwan a duk faɗin Jihar Kano, tare da ƙarfafa cigaba da haɗin kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsari da zaman lafiya yayin bukukuwan.







