Mai Shari’a Maryam Sabo ta Babbar Kotun Jihar Kano da ke zaman ta a Kano ta yanke wa wata mata mai suna Ebonine Rita Uzoamaka hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bisa laifin karɓar kuɗi har naira miliyan biyar da dubu ɗari shida (N5,600,000.00) ta hanyar yaudara.
Hukumar Binciken Almundahanar Kuɗi (EFCC) ta gurfanar da Uzoamaka a kotu a ranar 18 ga Agusta, 2021 kan tuhume-tuhume guda biyar na almundahanar kuɗi da suka kai jimillar N5,660,000.00.
Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce: “Ke Ebonine Rita Uzoamaka, a ranar 18 ga Janairu, 2021 a Kano, a ƙarƙashin ikon wannan kotu mai girma, da niyyar damfara, kin karɓi kuɗin Naira 2,000,000 (miliyan biyu) daga hannun Ochayi Anthony Eneche, wanda kika sa aka tura cikin asusun bankin ki mai lamba 0093030293 na Access Bank Plc, bisa ƙaryar cewa kina da katan 500 na D-Rich Baking Powder da za ki sayar masa, alhali kin san wannan magana ƙarya ce. Ta haka kika aikata laifin da ya saɓa wa Sashe na 1(1)(a) na Dokar Damfarar Kuɗi (Advance Fee Fraud) da Sauran Laifukan Damfara ta 2006, wanda Sashe na 1(3) na dokar ya tanadi hukuncin sa.”
Da farko ta musanta laifin (“ba ni da laifi”) lokacin da aka karanta mata tuhume-tuhumen, lamarin da ya sa aka shiga yin cikakkiyar shari’a.
A yayin shari’ar, lauyan masu ƙara, Salihu Sani, ya gabatar da ƙwararan hujjoji don tabbatar da laifin wadda ake tuhuma. Ya gabatar da shaidu guda huɗu tare da miƙa takardu da dama a matsayin hujja, waɗanda kotu ta amince da su a matsayin shaidu.
A ɓangaren kariyar ta kuwa, Uzoamaka kaɗai ce ta tsaya a matsayin shaida.

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Sabo ta same ta da laifi tare da yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru bakwai kan dukkan tuhume-tuhumen guda biyar.
Sai dai ta ba ta zaɓin biyan tarar dubu ɗari biyar (N500,000).
Ita dai Uzoamaka, ta samu wannan hukuncin ne bayan an kama ta da laifin karɓar naira miliyan 5.6 daga hannun wanda ta damfara, da sunan za ta samar masa da D-Rich Baking Powder daga Aba, Jihar Abiya.
Bayan karɓar kuɗin, ta kasa cika yarjejeniyar samar da kayan, maimakon haka ta karkatar da kuɗin don amfanin kan ta.
Daga bisani EFCC ta gurfanar da ita a kotu kuma aka same ta da laifi.







