Kamfanin Jiragen Sama na Saudiyya, wato Saudi Airlines, zai sake fara zirga-zirga daga Jidah zuwa Abuja a watan Yuni, ko kuma zuwa Janairu na 2027.
Jakaden Saudiyya a Nijeriya, Ambasada Yousef Bin Muhammed Al-Balawi, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a ofishin sa da ke Abuja.
Ya ce dawowar wannan zirga-zirgar za ta ƙara sauƙaƙa tafiye-tafiye tsakanin Nijeriya da Saudiyya, tare da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.








