Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cikakken goyon bayan sa ga sabon muƙaddashin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, domin ƙarfafa tsaro da maido da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Laraba a lokacin da yake naɗa Disu a Fadar Shugaban Ƙasa, yana mai jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban abin fifikon gwamnatin sa.
Tinubu ya buƙaci Disu da ya jagoranci rundunar ’yan sanda cikin adalci da ƙwarewa, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin shawo kan matsalolin ’yan bindiga, ta’addanci da sauran laifuffuka.

Ya ce gwamnatin sa za ta ba da cikakken tallafi da haɗin kai don tabbatar da nasarar sabon muƙaddashin IGP ɗin a wannan muhimmin aiki.







