• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Isar da saƙon gwamnati iri ɗaya shi ne ginshiƙin dawo da yarda daga jama’a — Minista

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 30, 2026
in Labarai
A A
0
Isar da saƙon gwamnati iri ɗaya shi ne ginshiƙin dawo da yarda daga jama’a — Minista
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabi a taron

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabi a taron

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada buƙatar gwamnati ta a riƙa yin saƙo iri ɗaya, daidaitacce, kuma wanda aka tsara shi da nufin samun amincewar jama’a, a matsayin muhimmin ginshiƙi na aiwatar da manufofin Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da Daraktocin Yaɗa Labarai da kuma Jami’an Yaɗa Labarai (RIOs) da ke kan matakin aiki na 14 zuwa 17 waɗanda ma’aikatar sa ta tura Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnati (MDAs).

Taron, wanda aka gudanar a Abuja, yana da taken: “Daidaita Bayanan Gwamnati da Shirin Sabunta Fata: Sake Gina Amincewa ta Hanyar Ingantacciyar Sadarwa ta Gaskiya da Bayyana Komai.”

Idris ya ce samun amincewar jama’a shi ne mafi muhimmancin jari a harkar sadarwar gwamnati, yana mai jaddada cewa dole ne jami’an yaɗa labarai su kasance masu tsare gaskiya da amana da kuma daidaito wajen gudanar da ayyukan su.

Ya ce: “Samun yardar jama’a shi ne mafi muhimmancin jarin mu. Da zarar an rasa yardar jama’a, to babu irin saƙon da za a yi wanda zai gyara shi.”

Ya yi gargaɗin cewa rarrabuwar saƙwanni da hanyoyin sadarwa daban-daban yana rage amince wa gwamnati sannan yana jefa jama’ar ƙasa cikin ruɗani, inda ya jaddada cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta riƙa yin magana da murya guda, bayyananniya kuma mai daidaito.

“Mu gwamnati guda ɗaya ce wadda ke yi wa muradin ƙasa ɗaya hidima, don haka dole ne saƙon mu ya nuna wannan haɗin kan,” inji shi.

Mahartan taron

Ministan ya buƙaci Jami’an Yaɗa Labarai da su ɗauki kan su a matsayin cikakkun abokan aiki a inda aka tura su aiki, ba wai ‘yan kallo kawai ba.

Ya ƙarfafa masu gwiwa da su riƙa hulɗa kai-tsaye da Ministoci, Manyan Sakatarori, da shugabannin hukumomi, yana mai cewa ƙwarewa da ƙwazo su ne ginshiƙan samun amincewa da tasiri.

Da yake magana kan ƙalubalen yaɗa labaran ƙarya da kuma saurin da kafofin sadarwa na zamani suke da shi, Idris ya jaddada muhimmancin isar da sahihin bayani cikin gaggawa, yana mai cewa jinkiri yakan bai wa labaran ƙarya damar su bazu.

Ko da yake ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na kare ’yancin faɗar albarkacin baki, ya ce dole ne a yi amfani da wannan ’yanci ta hanyar da ta dace.

Ministan ya kuma bayyana matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa ƙwarewa a tsakanin jami’an yaɗa labarai, ciki har da wajibcin bayar da rahotannin aiki a kai a kai, inganta tsarin tura ma’aikata, horaswa mai ɗorewa da ƙarin tallafin hukumomi.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta fara farfaɗo da Makarantar Horar da Jami’an Sadarwa ta Ƙasa (NIPI) domin haɓaka ƙwarewar jami’an yaɗa labarai na gwamnati.

A ƙarshe, Ministan ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai da mutunta juna, yana mai tunatar da mahalarta taron cewa su ne ginshiƙai wajen bayyana manufofi da nasarorin gwamnati, kuma dole ne su daidaita aikin su da muradun Shirin Sabunta Fata.

Daraktan Yaɗa Labarai a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Suleiman Haruna, yana gabatar da jawabi a taron

Taron ya samu halartar Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman; Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mista Ogbodo Chinansa Nnam; Darakta Janar na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali Muhammad Ali, wanda Babban Edita, Mista Mufutau Ojo, ya wakilta; Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; da Darakta Janar na Hukumar Gidajen Talbijin ta Ƙasa (NTA), Malam Salihu Dembos, tare da sauran manyan baƙi.

Teburin manyan baƙi a taron
Tags: MohammedIdrisShirinSabuntaFatayaɗalabarai
Previous Post

Hotuna: Ziyarar shugabannin kamfanin MTN zuwa hedikwatar CBN ta yi armashi

Next Post

Shettima ya halarci ɗaurin aurarraki a Kaduna

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Shettima ya halarci ɗaurin aurarraki a Kaduna

Shettima ya halarci ɗaurin aurarraki a Kaduna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!