Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda za a gudanar a birnin New York a watan Satumba, inda zai gabatar da jawabi ga shugabannin ƙasashen duniya.
Jakaden dindindin na Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce Tinubu ya tabbatar da cewa zai halarci taron yayin da yake amincewa da shirye-shiryen da Nijeriya ta yi domin halartar babban taron na bana.
“Shugaban Ƙasa ya tabbatar mana da cewa zai halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a watan Satumba,” inji shi.
Ibrahim ya ce Tinubu zai halarci wasu muhimman tarurrukan gefe na manyan shugabanni da za su mayar da hankali kan makamashi, ilimi da kuma gudanar da asibitoci.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasar zai yi amfani da wannan dama wajen bayyana wa ƙasashen duniya irin sauye-sauyen tattalin arziki da na shugabanci da gwamnatin Nijeriya take aiwatarwa.
Tinubu dai ya halarci zama na 78 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da kan sa, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilce shi a zaman na 79 da na 80.
Ambasada Ibrahim ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu zai tattauna da shugabannin duniya kan yadda za a ƙarfafa tsaron iyakokin ƙasashen Yammacin Afrika domin magance barazanar tsaro da ke ƙaruwa sakamakon iyakoki masu raunin tsaro.
Ya ce Nijeriya ta riga ta fara aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya kan wani shiri na tsaron iyakokin yankin, kuma za ta nemi ƙarin goyon bayan ƙasashen duniya yayin taron.
Za a buɗe zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 8 ga Satumba, yayin da muhawarar babban taron, inda shugabannin ƙasashe da gwamnatoci ke gabatar da jawaban su, za ta gudana daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba.
Ana sa ran taron na bana zai haɗa shugabannin duniya domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, cigaba mai ɗorewa, zaman lafiya da tsaro na ƙasa da ƙasa, da sauran manyan ƙalubalen da duniya ke fuskanta.







