• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Zargin kisan ƙare dangi: Nijeriya da Amurka suna tattaunawa ta hanyar diflomasiyya – Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 11, 2025
in Labarai
A A
0
Zargin kisan ƙare dangi: Nijeriya da Amurka suna tattaunawa ta hanyar diflomasiyya – Idris
Ana hira da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris a shirin "The World With Yalda Hakim" na gidan talbijin na Sky News

Ana hira da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris a shirin "The World With Yalda Hakim" na gidan talbijin na Sky News

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa hanyoyin diflomasiyya suna aiki yadda ya kamata wajen daidaita dangantaka tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka.

Idris ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin “The World With Yalda Hakim” na gidan talbijin ɗin Sky News da ke Birtaniya, inda ya ce, “An buɗe hanyoyin sadarwa, kuma zan iya tabbatar da hakan; muna magana da su, kuma ina ganin suna fara fahimtar halin da ake ciki. Muna ganin cewa yawancin bayanan da suke samu sakamakon rashin cikakkiyar fahimta game da bambance-bambancen da kuma sarƙaƙiyar matsalar da muke fuskanta.”

Ministan ya kuma danganta wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da aka haramta a Nijeriya da wasu masu neman goyon bayan gwamnati a Amurka, waɗanda ake zargin suna yaɗa bayanan ƙarya ga hukumomin Amurka.

Ya ce: “Ina so in bayyana cewa mun gano kai-tsaye akwai alaƙa tsakanin masu neman goyon bayan gwamnati a Amurka da wata ƙungiyar ta’addanci da aka haramta a Nijeriya. Mun kuma ga yadda suka kafa wannan gungun neman goyon baya a Amurka, suna tuntuɓar manyan jami’an gwamnati domin su taimaka masu wajen neman goyon bayan.”

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Amurka ta daɗe tana goyon bayan Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci, kuma yanzu ma ƙasar nan tana buƙatar irin wannan haɗin kai.

Ya ce: “Abin da muke faɗa shi ne, e, lallai muna da matsaloli a Nijeriya, muna da rikice-rikice da matsalolin tsaro, amma a baya gwamnatin Amurka ta taimaka wajen magance irin waɗannan matsaloli. Don haka, muna kira gare su da su sake haɗa kai da mu domin mu kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”

Ya bayyana cewa Nijeriya ta yi mamakin wasu bayanai da ke fitowa daga Amurka da matsayin su kan wannan batun, yana mai cewa dole ne ƙasashen duniya su fahimci yanayin musamman da Nijeriya take ciki.

Ya ce: “Muna son mu shaida wa duniya cewa abin da ake yaɗawa ba haka yake ba. Muna jin damuwar ‘yan ƙasa da kuma damuwar ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kan wasu kashe-kashen da ke faruwa, amma abin da muke nema yanzu shi ne fahimtar sarƙaƙiyar yanayin da muke ciki.”

Idris ya kuma yi shakku kan sahihancin bayanan da ake yaɗawa da ke nuna cewa ana nuna bambancin addini a Nijeriya, inda ya ce waɗannan bayanan “ba za su iya tabbatuwa ba idan an tantance su a kimiyyance.”

Ya tabbatar da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi ‘yancin addini, kuma ƙasar na ci gaba da kasancewa ƙasa mai addinai daban-daban duk da cewa wasu rikice-rikice suna faruwa, waɗanda ba su da nasaba da wariyar addini.

Tags: AmurkaDonald TrumpMohammed IdrisNijeriyaSky NewsYalda Hakimzargin kisan ƙare dangi
Previous Post

Tinubu ya taya Malam Shekarau murnar cika shekaru 70

Next Post

Manufar ƙarfafa jarin bankuna inganta tsarin hadahadar kuɗaɗe da bunƙasa ƙarfin tattalin arzikin ƙasa zuwa dala tiriliyan ɗaya – CBN

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa

Manufar ƙarfafa jarin bankuna inganta tsarin hadahadar kuɗaɗe da bunƙasa ƙarfin tattalin arzikin ƙasa zuwa dala tiriliyan ɗaya - CBN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!