• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Manufar ƙarfafa jarin bankuna inganta tsarin hadahadar kuɗaɗe da bunƙasa ƙarfin tattalin arzikin ƙasa zuwa dala tiriliyan ɗaya – CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 12, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

BABBAN Bankin Nijeriya (CBN) ya ce babbar manufar tilasta wa bankunan kasuwanci su ƙarfafa jarin su shi ne domin a ƙara inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe, ta yadda tattalin arzikin Nijeriya zai dangane zuwa dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030.

CBN ya bayyana haka a yayin da manya da ƙananan bankuna ke ci gaba da ƙoƙarin ganin sun cika sharuɗɗan mallakar adadin kuɗaɗen ƙarfin jarin da aka gindaya wa kowane banki a ƙasar nan.

Mataimakin Gwamnan CBN Mai Kula da Nagartar Tsarin Hada-hadar Kuɗaɗe, Philip Ikeazor, shi ne ya bayyana haka a yayin wani taron Kungiyar Manyan Manajojin Hulɗa da Jama’a na Bankuna.

Ikeazor ya bayyana wasu al’amurran kamar haka:

Wajibcin Bankuna Su Faɗaɗa Bai Wa Masu Ƙanana Da Matsakaitan Sana’o’i Lamuni: Ya ce hakan hanya ce da za ta ƙara samar da aikin yi da kuma hada-hadar kasuwancin da zai ci gaba da bunƙasa tattalin arziki.

Ƙara Yawan Masu Buɗe Asusun Ajiyar Kuɗaɗe Kuɗaɗe: Akwai buƙatar ci gaba da ƙara yawan masu ajiyar kuɗaɗe a asusun bankuna, musamman mata ta hanyar samar masu da damar kuɗaɗen Kasuwanci, musamman a yankunan karkara.

Dalilai Na Bunƙasa Jari A Fannin Fasahar Ƙirƙire-ƙirƙiren Zamani: Akwai buƙatar bunƙasa hada-hada a tsarin fasahar sadarwa da fasahar ƙirƙire-ƙirƙiren zamani, wato AI domin sauƙaƙa gudanar da ayyuka a ko’ina.

Saboda haka, Ikeazor ya ce ta hanyar da za a fi auna nasarar shirin ƙarfafa jarin bankuna shi ne samun nasarar waɗannan tsare-tsare.

Tun cikin ƙarshen watan Satumba ne dai CBN ya bayyana cewa bankuna 14 sun cika sharuɗɗan ƙarfin jarin Naira biliyan 500 da CBN ya gindaya.

A wancan lokacin, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa zuwa yanzu manyan bankuna 14 ne suka cika sharaɗin tabbatar da cewa ƙarfin jarin kowannen su kada ya gaza kai naira biliyan 500.

Cardoso ya bayyana haka ne a ranar, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwanaki biyu na Kwamitin Ƙwararrun Mashawartan Tattalin Arzikin Ƙasa, a Abuja.

Tun cikin watan Maris ne dai CBN ya kafa sharaɗin cewa duk wani babban bankin da ke da rassa a ƙasashen waje, tilas mafi ƙanƙantar jarin sa ya kasance Naira biliyan 500 lakadan ba ajalan ba.

A taron na ranar Talata, wanda shi ne na 302 da CBN ya shirya, tun bayan kafa bankin, Cardoso ya yi kira ga bankunan kasuwanci su ci gaba da hoɓɓasan ƙarfafa jarin su, domin kai ga nasarar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Har ila yau a wurin taron dai Babban Bankin Nijeriya ya rage kuɗin ruwan da bankuna ke caza daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.

CBN ya bayyana rage kuɗin ruwa, daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.

Mista Cardoso ne ya bayyana haka a ranar Litinin jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Ƙwararrun Bada Shawarwari kan Tattalin Arziki (MPC), a Abuja.

Ya ce kwamitin ya amince a rage kuɗin ruwa da ɗigo .50, wato daga kashi 27.5 bisa 100, ya koma kashi 27 bisa 100.

Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.

Gwamnan ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba saukar malejin tsadar rayuwa da na hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ake samu a jere.

Da ma masara sun yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.

Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki.

Wannan ragin kuɗin ruwa da CBN ya yi wanda bankuna za su riƙa cajin masu karɓar ramce, ya zo ne daidai lokacin da ita kuma Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar 2025, idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Nijeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja, a ranar Litinin.

Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025.

Zuwa cikin watan Nuwamba ɗin nan ana ƙara samun yawan bankunan da ke cika sharuɗɗan ƙarfafa yawan jarin su. Ko cikin makon da ya gabata sai da CBN ya shawarci bankunan da ba su iya cika sharuɗɗa su haɗe da wasu wato su yi maja domin ƙarin ƙarfi, ko kuma su rage ƙarfin gejin lasisin su.

A ƙa’ida dai CBN na so manyan bankuna masu rassa a ƙasashen waje ya kasance ƙarin jarin kowannen su ya kai naira biliyan 500. Su kuma manyan bankunan da iyakar ƙarfin su cikin gida ne, to kada ƙarfin jarin su ya gaza kai naira biliyan 200.

Tags: bankunaCBNOlayemi CardosoPhilip Ikeazor
Previous Post

Zargin kisan ƙare dangi: Nijeriya da Amurka suna tattaunawa ta hanyar diflomasiyya – Idris

Next Post

Kashim Shettima ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Ministan Yanayi

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Kashim Shettima ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Ministan Yanayi

Kashim Shettima ya je ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Ministan Yanayi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!