Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa ma’aikatar sa za ta ba Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC) cikakken goyon baya a ayyukan ta.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban hukumar, Dakta Aminu Yusuf, tare da Darakta-Janar na hukumar, Dakta Osifo Tellson Ojogun, a ofishin sa, a jiya Laraba.
Ministan ya ba su tabbacin cikakken goyon baya domin tabbatar da nasara, yayin da suke ƙoƙarin sake farfaɗo da hukumar domin ta zama mai tasiri da inganci wajen aiwatar da ayyukan ta.








