Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas ta fara bincike kan mutuwar wata yarinya ‘yar shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, wadda ake zargin mai kula da ita ta caka mata wuƙa har ta mutu a garin Rumueme, Ƙaramar Hukumar Obio/Akpor ta jihar.
Babu cikakken bayani kan lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, a lokacin tattara wannan rahoto.
Duk da haka, an samu labarin cewa mai kula da yarinyar ta kashe kan ta bayan ta gane girman abin da ta aikata.
Wata majiya ta ce ‘yar aikin ta je makarantar ɗiyar masu gidan ta, ta ɗauko ta, ta kai ta gida sannan ta aikata laifin.
A wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a, kakakin rundunar ’yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ta ce mahaifiyar yarinyar, Glory Joseph, ita ce ta kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.
Kakakin ta ƙara da cewa yarinyar ta rasu kafin a kai ta asibiti, inda ‘yar aikin – wadda ita ma ta kashe kan ta – aka tabbatar da mutuwar ta.
Ta ce an ajiye gawarwakin waɗanda abin ya ritsa da su a asibiti, kuma an miƙa wa Sashen Binciken Manyan Laifuka da Sashen Basirar Leƙen Asiri (SCID) na rundunar domin zurfafa bincike.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce, “A yau, 25 ga Nuwamba, 2025, wata Glory Joseph, mace, mai zama a lamba 21, Titin Okabia, Agip Estate, Rumueme, ta kai rahoto a ofishin cewa ’yar ta, Alicia Olajumoke, mace, mai shekaru bakwai, an caka mata wuƙa har ta mutu da misalin ƙarfe 14:00, ta hannun wata Success, mace, sunan ta na ƙarshe ba a sani ba tukuna.
“Ta kuma ce mai laifin ta je makarantar marigayiyar, ta ɗauko ta, ta mayar da ita gida, sannan ta caka mata wuƙar har ta mutu. Sannan ta caka wa kan ta wuƙa a maƙogwaro.
“An ziyarci wurin da abin ya faru, an ɗauki hotuna. An garzaya da marigayiyar asibiti inda aka tabbatar da mutuwar ta. Haka kuma an garzaya da mai laifin zuwa wani asibiti, inda ita ma aka tabbatar da mutuwar ta.
“An ajiye gawar marigayiyar a ɗakin ajiye gawa domin yin binciken likita. An miƙa shari’ar zuwa SCID. Bincike na farko yana gudana, za a sanar da ci gaba daga baya.”
Batun hare-haren da ake yi wa yara ta hannun ‘yan aiki ba su da yawa amma sukan faru a Nijeriya, lamarin da ke haifar da damuwa kan tantancewa da kulawar da ake yi wa masu aikin.
A wani labari irin wannan, an yanke wa wata ‘yar aiki hukuncin kisa ta hanyar rataya a cikin 2023 saboda kashe wata tsohuwa da ’yar ta da ta yi.







