Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Buhari, ta ce marigayi mijin ta, wato tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya sha fama da matsalar rashin isasshen abinci (malnutrition) na tsawon lokaci, lamarin da ya shafi lafiyar sa a lokacin da yake shugaban ƙasa.
Ta kuma ce wasu mutane masu ƙarfi da ke aiki tare da shugaban ƙasar, waɗanda ake kira ‘yan kabal, sun gurɓata tunanin sa a game da ita, har ta kai ga tsohon shugaban ƙasar ya fara kulle ƙofar ɗakin sa domin hana ta samun damar shiga wurin sa.
Waɗannan bayanai na daga cikin abin da ke cikin littafin From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda Dakta Charles Omole ya rubuta, aka kuma ƙaddamar da shi ranar Litinin a Cibiyar Taron Fadar Gwamnati (State House Conference Centre), Abuja.
Littafin ya ambato uwargidan tsohon shugaban ƙasar tana cewa matsalar rashin lafiyar da mijin ta ya fuskanta a 2017 ba ta samo asali ne daga wata cuta mai ban mamaki ko wata maƙarƙashiya ta ɓoye ba.
A cewar ta, matsalar ta fara ne da rushewar wani tsari na yau da kullum — “abinci na,” wato tsarin abinci da kari (supplements) da ta daɗe tana kula da su a Kaduna kafin su koma Aso Villa.
Littafin ya ƙara da cewa: “Lokacin da tsarin shugabanci ya mamaye rayuwar su ta sirri, ta ce ta zauna da manyan ma’aikatan da ke kula da shi kai-tsaye (likita, CSO, mai kula da gida) har ma da Darakta-Janar na DSS, a wani taro na ƙarshe. Ta bayyana musu tsari: a kullum, a lokuta na musamman, a kawo kofuna da kwanuka masu ɗauke da garin bitamin da mai, a ƙara ɗan sinadarin furotin a nan, a sauya hatsi a can. Jikin tsofaffi na buƙatar kulawa mai laushi da daidaito.”
Ta ƙara da cewa: “Muna zaune ne karo na farko kuma na ƙarshe,” inji ta. “Ba shi da wata cuta mai tsanani. A wannan shekaru, ana kula da su kamar yaro; garkuwar jiki ba iri ɗaya ba ce. A ƙara wannan, a cire wancan. A kiyaye lokaci. Ta bayyana musu dogon yaƙin da mijin ta ya sha da alamomin rashin isasshen abinci, da yadda ta shafe shekaru tana amfani da kari don daidaita abincin sa.”
“Daga nan,” a cewar ta, “aka fara yaɗa ji-ta-ji-ta da tsoratarwa. Waɗannan ma’aikatan na kusa da shi suka fara dasa tunani da shakku a zuciyar mijin ta. ‘Sun ce ina son kashe shi.’ Ta fi bayyana rauni fiye da fushi yayin da take tunawa da lamarin, amma matakan da suka biyo baya ba su kasance na tsaka-tsaki ba.
“Wataƙila waɗannan ba ayyuka na yau da kullum ba ne,” ta yi tunani. “Miji na ya yarda da su na tsawon kusan mako guda,” inji ta. “Ya fara kulle ɗakin sa, ya sauya wasu ƙananan halaye.” Kuma kicin, zuciyar tsarin, ya fita daga tsari. Ana jinkir ta abinci ko a rasa shi gaba ɗaya, an kuma dakatar da kari (da aka yi amfani da su tsawon shekaru, inji ta).”
An bayyana cewa Buhari, wanda mutum ne siriri kuma ba ya yawan cin abinci sosai ko da a lokutan da yake cikin ƙoshin lafiya, ya fara rage nauyi. “Tsawon shekara guda, bai ci abincin rana ba,” inji A’isha.
“Yana da tsarin rayuwa. Sun lalata masa tsarin abinci,” A’isha ta yi iƙirarin cewa mijin ta ya daɗe yana fama da rashin isasshen abinci tun fiye da shekaru shida kafin ya shiga Villa. Ta kula da abincin sa a tsanaki; bitamin a nan, kari na gina jiki a can. Sakamakon haka, an kafa tsari mai kyau da tasiri, wanda ya kiyaye shi cikin ƙarfi da ƙoshin lafiya.
“Amma,” inji ta, an faɗa mata cewa Buhari yanzu ‘Dukiyar Ƙasa’ ne, ba mijin ta kaɗai ba; saboda haka aka yi watsi da tsarin da take bi, sannan tawagar masu kula da shi a Villa (da masu goyon bayan su) suka ɗauki tasu hanyar.”
Hajiya A’isha Buhari ta ce ba a ba mijin ta guba ba kamar yadda ake yaɗa ji-ta-ji-ta a wasu wurare, kuma babu wani zazzaɓi ta ban-mamaki da ke ɓoye a cikin hanyoyin iska; matsalar sa ita ce an lalata tsarin abincin sa kuma an yi masa rashin kulawa sosai.
Ta ce lokacin da aka gaggauta kai Buhari London, likitoci sun rubuta masa wani tsari na kari mafi ƙarfi fiye da wanda ita take ba shi.







