An gudanar da taron Shugabannin Kungiyoyin Masu Zuba Jari na Amurka da Afrika, domin bunƙasa kasuwanci da zuba jari tsakanin Amurka da Nijeriya, wanda aka gudanar a Washington, D.C.
A taron da aka shirya ranar Litinin, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya gana da manyan shugabannin kasuwanci da masu zuba jari na duniya domin bayyana sabon tsarin da fasalin tattalin arzikin Nijeriya, mai cike da tsari, ƙa’idoji da kuma ƙudirin ƙasar na samar da tattalin arziƙi mai sauƙin yi wa kyakkyawan fata nagari lamiri.
Kamar yadda ya yi bayani, Cardoso ya ce tsarin tattalin arzikin Nijeriya abin ɗauka da muhimmanci ne sosai, abin gaskatawa, ba tare da wani shakku ko tababar makomar sa ba. Ya ce CBN na jan ragamar tattalin arzikin Nijeriya bisa wasu ƙa’idoji da dokokin da aka shimfiɗ, ta yadda maso zuba jari daga sassan duniya za su gamsu da fa’idojin zuba jari a ƙasar.
A wannan lokaci da masu zuba jari a duniya ke nuna taka-tsantsan tare da neman tabbaci a cikin sauye-sauyen yanayin kasuwanci na duniya, Gwamna Cardoso ya sake jaddada ƙudirin Nijeriya na bin manufofi bisa ƙa’ida, tsarin kasuwanci managarci mai bin turba sahihiya, kuma mai cike da ingantattun tsare-tsaren hukumomi suka bijiro da su.
Ya yi nuni da cigaban da aka samu a gyaran tsarin musayar kuɗaɗen waje, aiwatar da manufofin kuɗi na game-gari, gyaran tsarin hadahada a bankuna da zamanantar da tsarin biyan kuɗi a matsayin muhimman ginshiƙai na dawo da amincewa da kuma samar da ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa, wanda ɓangaren masu zaman kansu ke jagoranta.
Taron, wanda Cibiyar Kasuwanci ta Amurka–Afrika (U.S.–Africa Business Center) ta Ƙungiyar Kasuwanci ta Amurka (U.S. Chamber of Commerce) ta shirya a ranar Litinin, 15 ga Disamba, ya samar da dandali na musamman don tattaunawa kan samar da daidaiton gagarumin tattalin arziki, fayyace dokoki da ƙa’idoji da kuma damar faɗaɗa ayyukan da za a iya zuba jari a cikin su a muhimman sassa. Sai kuma ƙarfafa sabon mataki na zurfafa hulɗar kasuwanci tsakanin Amurka da Nijeriya.
Kamar yadda Kendra Gaither, Shugabar Cibiyar Kasuwanci ta Amurka–Afrika a Ƙungiyar Kasuwanci ta Amurka ta bayyana:
“Abin da masu zuba jari ke gamsuwa a yau shi ne bayyananniyar fahimtar ƙa’idoji masu tsari, gyare-gyare masu inganci, da tabbatar da gaskiya wajen aiwatar su.
“Saƙon Nijeriya yana ƙara gamsar da masu zuba jari, kuma wannan yana da matuƙar muhimmanci a tattalin arzikin duniya da ke neman ganin ta aminta da shi, domin gamsuwa da kyakkyawan hasashen ɗorawa,” inji ta.
Taron wanda ya gudana a ƙarshen shekarar 2025, ya zo daidai lokacin da CBN a ƙarƙashin Cardoso ya shafe shekaru biyu cur yana bijiro da tsare-tsaren gina ƙasa da bunƙasa samuwar arziki, ta yadda masu zuba jari za su amince da irin tsarin hadahadar kuɗaɗe ta tafiya a ƙasar nan.
A ƙoƙarin sa na saisaita tattalin arziki, CBN ya fito da tsarin ƙarfafa jarin manya, matsakaita da ƙananan bankuna, an saisaita darajar naira a kasuwar hadahadar musayar kuɗaɗen waje, ya kafa wa bankuna ƙa’idoji, ya gindaya wa cibiyoyin kuɗaɗe masu POS sabbin sharuɗɗa, kuma kwanan nan CBN ya soke lasin wasu bankuna biyu da suka karya ƙa’idoji da kasa cika sharuɗɗa.






