• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Rahoton Musamman

Yadda Tsarin Musayar Kuɗaɗen Waje Na Gwamnatin Tinubu Ya Ƙarfafa Darajar Naira A Hada-hadar Kayan Da Ake Fitarwa Daga Najeriya Zuwa Ƙasashen Waje

TANIMU YAKUBU by TANIMU YAKUBU
September 1, 2025
in Rahoton Musamman
A A
0
Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba – Idris
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rushe tsarin musayar kuɗaɗen waje da ya zame wa tattalin arziki ƙarfen-ƙafa cikin 2024, sai masu sukar abin suka riƙa gaggawar cewa an karya darajar Naira ƙasa warwas. Domin a cikin watan Maris, 2024 sai da Dalar Amurka ɗaya ta kai Naira 1,800. Ai kuwa sai jaridu suka riƙa yayata cewa alƙadarin Naira ya karye, tana neman zama takardar tsire.

Amma masu wannan surutai su ba su san cewa gwamnati ta san abin da take yi ba ne. Saboda a ƙarƙashin ƙasa ta tabbatar cewa tsarin da ta ɗauka, zai ƙarfafa darajar Naira yadda za ta riƙa gogayya da manyan kuɗaɗen duniya. Kamar dai yadda muke gani a yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.

Zuwa watan Agusta 2025, har Naira ta samar wa kan ta darajar kashi 15.28%, a gogayyar gwada ƙarfin ƙwanjin da ta yi da Dalar Amurka, a hada-hadar cinikayyar fitar da kaya ƙasashen waje daga Najeriya. Saboda a cikin watanni biyar bayan shigo da tsarin, Dala ta sauka ta koma Naira 1,525. Wato kusan kashi 48.9% kenan a shekara. A kula cewa tsarin da gwamnatin Tinubu ta shigo da shi ne ya haifar da haka. Ba kawai kaciɓus aka fara samun wannan nasara ba.

Tsarin ya haifar da bunƙasa da ƙaruwar kuɗaɗen fetur da dangogin sa, yawan kuɗaɗen da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke turowa cikin gida ya ƙaru, kuma aka warware cikas ɗin matsalar musayar kuɗaɗe ta Dala biliyan huɗu ($4b) duk a cikin watannin biyar. Kawar da wannan matsala kuma ta kwantar da ran masu shawarar zuba jari a Najeriya, sun daina fargabar da suke yi wa Naira.

Haka kuma shigo da tsarin musayar kuɗaɗen waje na bai-ɗaya da aka yi, ya samar da sahihiyar kasuwar hada-hadar musayar kuɗaɗe, inda kowane kuɗi ke goyayyar samar wa kansa daraja ta haƙiƙa.

Shin me ya sa hakan ke da muhimmanci? Saboda tsarin musayar kuɗaɗe na gaskiya da gaskiya yana faranta ran masana tattalin arziki, sannan yana canja badalin alƙakuman cinikayya.

Sai aka wayi gari aka daina yanka wa kayayyakin da ake fitarwa daga Najeriya farashi na shaci-faɗi, saboda da hasashen ƙarfin da ake wa Naira, sai ya kasance ana sayen komai da daraja. Buhu ɗaya na riɗi ko ‘cocoa’ da irin su cakulan suka yi arha a biranen New York, Mumbai ko birnin Sao Paulo, Amma kuma nan a gida Najeriya darajar su ba ta karye ba, ballantana a ce manomi da masu masana’antu sun rage samun kuɗi.

To wannan kyakkyawan sakamako ya yi fa’ida sosai. Domin an samu ƙarin kuɗaɗe daga cinikin kayayyakin da ba fetur ba da ake fitarwa waje, daga Dala biliyan 2.696 a Watanni Shidan Farkon 2024 zuwa Dala biliyan 3.225 a Watanni Shidan Farkon Shekarar 2025. Wato ƙarin kashi 19.62% kenan. Wannan fa ba hasashe ko kirdadon farashi ba ne. Domin an samu ƙarin yawan kayayyakin da ake fitarwa daga Najeriya, metrik tan miliyan 3.83 zuwa metrik tan miliyan 4.04, wanda hakan hujja ce mai nuna cewa masu sayen kayayyakin Najeriya daga ƙasashen waje suna saye fiye da farashin can baya. A lokaci ɗaya kuma suna sayen ƙarin kaya da yawan gaske. Magana kenan!

Tsari Ya Yi Kyau, Kowa Ya Samu Yadda Yake So:

  • Masu Sayen Kayayyakin da Najeriya ke fitarwa waje na samun kaya da arha fiye da arhar na wasu ƙasashe.
  • Masu fitar da yayayyakin sayarwa daga Najeriya na murnar ƙaruwar darajar Naira, wanda hakan ya samar da ƙarin masu zuba jari a hada-hadar ‘cocoa’ ana sarrafa shi zuwa cakulan da masu sarrafa riɗi suna ɗura man sa cikin kwalabe.
  • Kayayyakin sayarwar da Najeriya ke fitarwa sun ƙara wa tattalin arziki ƙarfin samun ƙarin maƙudan shigowar kuɗaɗe a hada-hadar musayar kuɗaɗe. Ya ƙara wa Naira ƙarfin ƙwanji, ba tare da an rage mata karsashin iya yin gogayya da kuɗaɗen waje ba.

Ƙarin Bayani Dalla-dalla:

1. Sabon Tsarin Musayar Kuɗaɗen Waje ya samar da sahihiyar darajar Naira.

2. Arhar Farashin Kaya a Dalar Amurka ya samar da Bunƙasar Adadin Kayan da ake Fitarwa.

3. Yawan Kayan da ake Fitarwa ya samar da Ƙarin Yawan Shigowar Kuɗaɗen Waje Cikin Najeriya.

4. Ƙarin Yawan Kuɗaɗen Waje Cikin Najeriya ya haifar da Daidaiton Darajar Naira.

5. Daidaiton Darajar Naira ya samar da Yarda da Aminci a Zukatan Masu Zuba Jari da kuma Samar da Ci-gaba Mai Ɗorewa.

Abin sha’awa a waɗannan matakai shi ne a tare da juna suke ko yaushe. Yayin da kayayyakin da ake fitarwa daga Najeriya ke ƙara samun tagomashi da nasibi a kasuwannin duniya, ƙarin yawan shigowar maƙudan daloli ya ƙarfafa darajar Naira. To wannan kuwa ya matuƙar rage shakkun da masu zuba jari ke yi wa tattalin arzikin Najeriya sosai. Ga shi kuma za a ci gaba da kwararar zuba jari, ta yadda kuɗaɗen asusun ajiyar kuɗaɗen waje zai riƙa cika maƙil.

Waɗanda suka sukar wannan tsari da farko har suna cewa “naira ta koma takardar tsire”, ba su fahimci tsarin ba ne kwata-kwata: sakin Naira a kasuwa domin ta samar wa kan ta daraja ba alama ce ta karya mata ƙarfi ko daraja ba. A’a, makami ne dai na bata dama domin ta yi gogayya da manyan kuɗaɗen duniya har ƙasa ta yi tsere da sauran ƙasashe a fannin tattalin arziki.

Saboda haka gwamnatin Tinubu ta hau gwadaben tattalin arziki mai ɗorewa, wanda ke samar da ci gaba ta hanyar kuɗaɗen shiga daga kuɗaɗen cinikayyar kayan da ake fitarwa waje.

Idan Najeriya ta ɗore bisa wannan gwadabe, farfaɗowar darajar Naira ba a fannin musayar kuɗaɗe kaɗai zai dogara ba, zai kasance magana ake ta yadda tattalin arziki zai maida Naira makamin da Najeriya ke amfani wurin gogayya a kasuwannin duniya.

* Yakubu shi ne Babban Darakta, Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya

Previous Post

Kalmomin Hausa 170 Masu Asali Daga Larabci

Next Post

Dalla-dalla: Yadda Yankin Arewa Maso Yamma Ya Fi Sauran Yankuna Samun Manyan Ayyukan Raya Ƙasa A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu

Related Posts

Rahoton Musamman

Taƙaitaccen Tarihin Ɗanwaire Da Ƙasar Ruma

September 16, 2026
D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika
Rahoton Musamman

D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika

July 3, 2026
Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya
Rahoton Musamman

Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya

June 11, 2026
Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas
Rahoton Musamman

Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas

May 26, 2026
Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi
Rahoton Musamman

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

May 14, 2026
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

March 24, 2026
Next Post
Dalla-dalla: Yadda Yankin Arewa Maso Yamma Ya Fi Sauran Yankuna Samun Manyan Ayyukan Raya Ƙasa A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu

Dalla-dalla: Yadda Yankin Arewa Maso Yamma Ya Fi Sauran Yankuna Samun Manyan Ayyukan Raya Ƙasa A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!