Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru Maude, ya fara ziyarar ƙoƙarin inganta haɗin kai tsakanin ɓangaren shari’a da hukumomin EFCC da na Kula da Gidajen Gyaran Hali a Jihar Kano.
A ziyarar da ya fara kai wa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ofishin Yankin Kano, tattaunawar da suka yi ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, inganta musayar bayanai da ƙarfafa haɗin kai wajen bincike da gurfanar da masu aikata laifukan kuɗi da tattalin arziki.
Maude ya jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano da EFCC wajen inganta gaskiya, riƙon amana da tabbatar da doka.
Ya tabbatar da shirye-shiryen ma’aikatar na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar, domin tabbatar da ingantacciyar gurfanarwa da adalci.
Daraktan EFCC na Yankin Kano ya yaba da ziyarar tare da tabbatar wa babban lauyan ci gaba da haɗin kai da ma’aikatar.
A ci gaba da ziyarar, Maude ya kai ziyara a Hukumar Kula Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya da Gidan Gyaran Hali na Dawakin Tofa.
Ziyarar ta bada dama wajen duba yanayin aiki, tattaunawa da jami’an gyaran hali da kuma tattauna batutuwan jin daɗin fursunoni, samun adalci, da rage cunkoso a gidajen tsare masu laifi.
Maude wanda babban lauya ne (SAN), ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na aiwatar da sauye-sauyen ɓangaren shari’a da ke fifita kare haƙƙin ɗan Adam, hanzarta shari’a, da inganta harkokin gidajen gyaran hali bisa dokokin ƙasa da ƙa’idojin duniya.







