• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya ceto tattalin arzikin Nijeriya cikin shekaru biyu – Cardoso

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 30, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ya ceto tattalin arzikin Nijeriya cikin shekaru biyu – Cardoso
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yana jawabi a dinar Cibiyar Manyan Masu Hannu a Harkokin Banki ta Nijeriya (CIBN), ranar Alhamis a Legas.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yana jawabi a dinar Cibiyar Manyan Masu Hannu a Harkokin Banki ta Nijeriya (CIBN), ranar Alhamis a Legas.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana irin gagarumar nasarar farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya da ya ce an samu daga hawan sa shugabancin bankin zuwa yanzu a ƙarshen 2025.

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi wurin taron cin abincin dare na shekara-shekara na Cibiyar Manyan Masu Hannu a Harkokin Banki ta Nijeriya (CIBN), ranar Alhamis a Legas.

A wurin taron, wanda shi ne na 60, Cardoso ya jaddada cewa, “A daren yau, mun hallara a wani muhimmin lokaci ga ƙasar mu, wanda a daidai lokacin da duniya ke da rashin tabbas, lokacin da ake sake fasalin manufofi a gida, da lokacin da ake ci gaba da farfaɗo da muhimman cibiyoyi.

“Duk da ƙalubalen da ke fama da su da waɗanda ake fuskanta, mun samu sabon haske. A cikin shekarar da ta gabata mun dage wajen dawo da daidaiton tattalin arziki, gina amincewa, da ƙarfafa martabar Babban Bankin Nijeriya.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa mun samu ci gaba mai ma’ana a waɗannan fannoni, duk kuwa da cewa muna sane da har yanzu akwai sauran ƙalubale a gaban mu.

“Mun tsaya kan abin da muka faɗa tun a farko. Wato abin da muka ce za mu yi, shi muke yi bisa tsari na gaskiya da daidaito.”

Ya tunatar da matsalolin da al’umma da dama ke fuskanta a yanzu, inda ya ce, “Abubuwan da suka faru kwanan nan da kuma maida hankalin duniya kan batun tsaro, sun nuna mana tasirin da rikice-rikice ke yi ga mutane.

“A madadin Babban Banki, muna miƙa ta’aziyyar mu ga iyalai da al’umma da abin ya shafa.

“Ko da yake harkar tsaro ba ta cikin hurumin Babban Banki, amma muna sane da illolin ta ga tattalin arziki. Gwamnati na ɗaukar matakai, mu kuma a matsayin na masu kula da samar da daidaito a cikin kuɗi, muna tabbatar da cewa asasin tattalin arzikin ƙasa ya tsaya da ƙarfi domin zuba jari, rayuwar jama’a, da juriya su ci gaba da ƙarfafa yayin da ake ci gaba da shawo kan matsalolin tsaro.”

Cardoso ya fahimtar dangane da cigaban Nijeriya a yau, inda ya ce tilas ne mu duba matsayin tattalin arzikin duniya, wanda ya ce yana tafiya cikin rauni saboda, rikice-rikicen siyasa, haka kuma ƙasashen masu ƙarfin arziki sun shiga yanayin raguwa, yayin da ƙasashe masu tasowa da dama, musamman a Afrika, ke fama da tsadar kuɗin waje da hauhawar farashi.

Ya ci gaba da munin cewa duk da wannan, akwai wuraren da aka samu sauƙi saboda raguwar darajar Dalar Amurka da saukar hauhawar farashi. Ƙasashe da dama a Afrika sun fara samun kwanciyar hankali a kuɗin su. Bugu da ƙari, Afrika ta Sub-Sahara na sa ran yin ci gaba da kashi 3.8% a 2025 da kashi 4.4% a 2026.

“Nijeriya, Habasha, da Côte d’Ivoire na jagorantar wannan farfaɗowa, sakamakon ingantattun tsare-tsaren gida, ƙarfaffun cibiyoyi, da ingantaccen shugabanci,” inji shi.

Daga Ina Zuwa Ina?

Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da muka hau muƙami, Nijeriya na cikin matsaloli masu tsanani, kama dsga hauhawar farashi na tashi, ga shi a lokacin an yi fama da ƙarancin Dala a bankuna.

“Sannan akwai rashin amincewa ga manufofin tattalin arziki. Kuma an kauce daga tsarin kuɗi na zamani. Sannan shigo da kuɗi daga ɓangaren masu sha’awar zuba jari cikin Najeriya ya tsaya cak. Ita ma kasuwar musayar kuɗi ta durƙushe.

“Akwai kwantai na bashin biyan buƙatun masu neman dala sama da dala biliyan 7 da ba a biya ba. Tazarar farashin naira a kasuwannin hukuma da na bayan fage ta wuce zuwa fiye da kashi 60%.

“Hauhawar farashi ya kai kashi 34.6% a Nuwamba 2024. Farashin abinci ya matse al’umma, har an shiga ƙuncin rayuwa.”

Cardoso ya ce, “Wannan shi ne halin da muka samu Nijeriya, ba a bakin rami ba, amma a ciki tsundum.

Yadda Muka Ceto Tattalin Tattalin Arzikin Nijeriya

Ya bayyana cewa cikin shekara guda, komai ya fara canzawa, yayin da ƙarfin tattalin arzikin cikin gida ya tashi zuwa kashi 4.23% a cikin watanni ukun tsakiyar shekarar 2025. Wannan kuwa shi ne mafi girma cikin shekaru huɗu.

“Hauhawar farashi ta ragu daga 34.6% zuwa 16.05% a Oktoba 2025, inda watanni bakwai a jere tsadar da hauhawar na raguwa.

“Hakan na dawo da ƙarfi da nauyin aljihun jama’a ya dawo har ake iya sayen kayayyakin biyan buƙatu na yau da kullum.

“Manufar mu ita ce mu ci gaba da rage hauhawar farashi. Mun inganta bayanai, mun ƙarfafa sadarwa, mun daina biyan gibin kuɗi ga gwamnati. A shekarar 2026 ana sa ran ci gaba da saukar farashi.

“Gyaran kasuwar hadahadar kuɗaɗen waje na daga cikin gyare-gyaren da Cardoso ya ce ya yi tasiri sosai wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan.

“Mun wargaza tsofaffin hanyoyi da dama. Mun biya dukkan bashin kuɗaɗen waje ga masu neman musayar kuɗi na baya. An kafa dokar musayar kuɗaɗe, domin inganci da gaskiya.

“Naira yanzu tana cikin daidaitaccen matsayi, ta yadda tazarar ta da kasuwar bayan fage tana ƙasa da kashi 2%. Jarin waje ya kai dala biliyan 20.98 cikin watanni 10 na 2025.”

Gwamnan ya sake tabbatar da cewa adadin kuɗin ajiyar waje ya kai Dala biliyan 46.7, wato mafi girma cikin kusan shekaru bakwai. Wannan ya zo ne ba ta hanyar basussuka ba, sai dai ta hanyoyin cikin gida da ƙaruwar fitar da kayayyakin da ba na mai ba.

Ya ce a ƙoƙarin da CBN ke yi domin bunƙasa tattalin arziki ya kai geji da mizanin Dala tiriliyan ɗaya nan da 2030, tuni har an samu bankuna 16 waɗanda suka cika sharuɗɗan ƙara ƙarfin jarin su.

Tags: bankunaCBNCIBNdinanasaroriOlayemi Cardoso
Previous Post

Sojoji sun ceto ‘yan mata 12 da aka sace a Borno

Next Post

Babu wani kisan gilla a Nijeriya, inji Bishop Kukah

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Babu wani kisan gilla a Nijeriya, inji Bishop Kukah

Babu wani kisan gilla a Nijeriya, inji Bishop Kukah

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!