Babban Bishop na Roman Katolika na Diyosis na Sokoto kuma Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, Rabaran Matthew Kukah, ya bayyana cewa ba a samun kisan kiyashin Kiristoci a Nijeriya.
Yayin da yake jawabi a taron ƙoli na 46 na Knights of St. Mulumba a Kaduna, Bishop Kukah ya ce alƙaluman da ake yaɗawa game da zargin kisan Kiristoci ba su cika sharuɗɗan da ake kira “kisan ƙare dangi” ba, kuma babu ingantattun bayanai da ke goyon bayan su.
Ya ce matsayin sa ya yi daidai da na Sakataren Harkokin Wajen Vatican, Shugaban Majalisar Bishof-Bishof Katolika ta Nijeriya, da dukkan bishop-bishop Katolika a ƙasar nan.
Ya ce: “Ana cewa wai ana ƙona coci 1,200 a Nijeriya a kowace shekara, sai na tambayi kai na, wace Nijeriyar ake nufi? Abin mamaki, babu wanda ya tuntuɓi Cocin Katolika domin samun sahihan bayanai. Ba mu san daga ina waɗannan alƙaluma suka fito ba.
“Duk waɗanda ke magana game da tsanantawa, akwai wanda ya taɓa kira ya tambaya, ‘Bishop Kukah, yaya al’amura suke?’ Bayan da ake yaɗawa suna kauce wa Cocin Katolika ne domin sun san Katolika ba su dogara da ji-ta-ji-ta.”
Bishop Kukah ya ce ma’anar kisan ƙare dangi tana dogara ne da niyya, ba kawai kan yawan waɗanda suka mutu ba.







