• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Manyan nasarori 25 da CBN ya samu cikin watanni shidan farko na 2026

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 29, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Babban Bankin Nijeriya tare da Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso (Hoton CBN daga shafin: Beautiful Nigeria)

Babban Bankin Nijeriya tare da Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso (Hoton CBN daga shafin: Beautiful Nigeria)

A farkon watan Janairu na wannan shekara ta 2026, na bayyana muhimman nasarori har guda 20 da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya samu a cikin 2025, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso. Yanzu kuma da 2026 ta zo tsakiya daidai, wato ƙarshen watan Juni, na yi ƙoƙarin fito da aƙalla nasarori 25 da CBN ya samu a cikin watanni shida kacal na wannan shekara:

1. Samun nasarar kammala Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna, wanda zuwa adadin jarin bankunan Nijeriya ya ƙaru da fiye da naira tiriliyan 4 a ƙarshen Maris, 2026.

2. Ɗaga darajar irin su Opay, Moniepoint, Palmpay zuwa cikakkun bankunan hadahadar kuɗi.

3. Tumbatsar asusun ajiyar kuɗaɗen waje zuwa dala biliyan 50.

4. Fito da tsarin magance yawan samun tangarɗa da matsalolin katin ATM da na’urorin ATM.

5. Yadda Tarayyar Turai (EU) ta bi sahun hukumar FATF, ta cire sunan Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ke da hatsarin safarar kuɗi.

6. Kafa Kwamitin PSPC, wanda zai sa-ido kan tsarin biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani.

7. Batun kafa kwamitin sulhu domin warware rikice-rikicen masu taurin-bashi a bankuna.

8. Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗin ajiyar kwastomomin bankuna.

9. Gindaya sharuɗɗa kan BVN domin tsaurara matakan kare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna.

10. Ci gaba da danne malejin hauhawar farashi domin hana shi cillawa sama.

11. Yabon da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙarfafa yawan jarin bankuna.

12. Shan laƙani da dafa’i masu ƙarfin hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana.

13. Ci gaba da gindaya ƙa’idoji da sharuɗɗan hana wasu bankuna raba ribar ƙarshen shekara-shekara, sanadiyyar ƙaƙudubar bashin naira tiriliyan 2.9 da suka bai wa Nestoil, bayan kamfanin ya kasa biyan kuɗin.

14. Gargaɗi da jan-kunne ga gwamnatocin jihohi tare da nuna masu illar ciwo bashin alaƙaƙai mai zame wa jihohi jangwangwama.

15. Ambaliyar masu zuba jari cikin Nijeriya, bayan sun yi amanna da nagartattun sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da CBN ya bijiro da su.

16. Ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje.

17. Samun jinjina da ƙarin daraja daga S&P, kamfanin tantace daraja ko naƙasun manufofin kuɗi na ƙasashen duniya.

18. Ƙin amincewa da kiraye-kirayen komawa tsohon tsarin bayar da tallafin lamuni.

19. Shirin rage yawan takardun naira da ke hannun jama’a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100, nan zuwa ƙarshen 2028.

20. Kafa wa bankuna sharaɗin riƙa bibiyar dalilin yadda kwastomomi ke tura kuɗaɗe daga asusun ajiyar su na kuɗaɗen waje.

21. Jinjina da yabon da Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya yi wa CBN, sakamakon nasarar shirin ƙarfafa jarin bankuna.

22. Yadda CBN ya haskaka birnin Landan da duniya yayin da bankin ya lashe Kyautar Gwarzon Babban Banki na Shekara.

23. Fitar da sabbin ƙa’idojin bayar da lasisi da sa-ido kan kamfanonin rukunin harkokin kuɗi (HoldCos).

24. Saisaita gejin ribar rancen dare ɗaya biya washegari da sassafe a tsakanin bankuna (NOFR).

25. Gaggauta kulle asusun ajiya da kadarorin waɗanda gwamnatin tarayya ta zarge su da tallafa wa ta’addanci.

Tabbas, idan aka yi nazari da la’akari da waɗannan nasarori 25 na wannan shekara tun a watanni shidan farko, alamomi na ci gaba da nuna yadda CBN ke ƙara jajircewa wajen shiga gaba kan ingantawa da bunƙasa tattalin arziki, a matsayin sa na jagoran bunƙasa tattalin arziki da tsare-tsaren manufofin kuɗi a Nijeriya.

Previous Post

Yadda CBN ke ƙoƙarin rage yawan tsabar kuɗi naira tiriliyan 5.2 da har yanzu ke hannun jama’a 

Next Post

Gagarumin garambawul: CBN ya ƙwace lasisin ƙananan bankuna 46 saboda kasa cika ƙa’idoji da sharuɗɗa

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

Gagarumin garambawul: CBN ya ƙwace lasisin ƙananan bankuna 46 saboda kasa cika ƙa’idoji da sharuɗɗa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!