• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

UNGA: Shettima ya tallata damar zuba jari na dala biliyan 200 a fannin makamashi a Nijeriya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 23, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
UNGA: Shettima ya tallata damar zuba jari na dala biliyan 200 a fannin makamashi a Nijeriya
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima yana jawabi ga membobin ƙungiyar BCIU a New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima yana jawabi ga membobin ƙungiyar BCIU a New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana wa masu zuba jari na ƙasashen waje cewa Najeriya na da damar zuba jari mai darajar sama da dala biliyan 200 a fannin makamashi.

Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Ƙungiyar Kasuwanci ta Ƙasa da Ƙasa (Business Council for International Understanding – BCIU) ta shirya a birnin New York, Amurka, gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.

Shettima ya ce Nijeriya na buƙatar haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin cin gajiyar wannan dama, musamman a fannonin makamashi na zamani.

Ya ce Nijeriya tana da mai da iskar gas mafi yawa a Afrika, da kuma hasken rana mai ƙarfi fiye da ƙasashe da dama a nahiyar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.

Kashim Shettima, sanye da dara a dama, a taron

Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch & Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi.

Shettima ya ce: “Najeriya ita ce babbar tattalin arzikin Afrika ta Yamma, kuma tana da kasuwa mafi girma a nahiyar, inda al’ummarta ke kaiwa miliyan 236 yanzu, ana sa ran za ta kai miliyan 320 nan da 2040.”

Ya bayyana cewa Nijeriya tana da matasa da yawa, sama da kashi 58 cikin ɗari ‘yan ƙasa da shekaru 30 ne, lamarin da ya ce ke baiwa ƙasar manyan haziƙai a fannoni daban-daban, ciki har da fasahar zamani.

Shettima ya yi kira ga masu zuba jari da su yi amfani da wannan damar, yana mai cewa Najeriya na kan gaba wajen zama cibiyar kasuwanci da kirkire-kirkire a nahiyar Afrika, tare da kasancewa babbar hanyar shiga kasuwar AfCFTA mai darajar dala tiriliyan 3.4.

A gefe guda, Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Olajumoke Oduwole, ta ce tun bayan shekarar 2023 gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki, kuma hakan ya fara kawo canje-canje da inganta halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Kashim Shettima tare da jami’an ƙungiyar bayan taron

Ta ce, “A halin yanzu, akwai fiye da dala biliyan 50 daga masu son zuba jari da aka tattara a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.”

Shettima ya yi wannan bayani ne jim kaɗan bayan ya halarci taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi na minti uku wajen tunawa da cikar majalisar shekara 80.

Tags: Kashim ShettimaUNGAƘungiyar Kasuwanci
Previous Post

Tattalin Arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23% a zango na biyu na 2025 – NBS

Next Post

Minista ya yaba wa NBTE kan bunƙasa ƙwarewar ƙirƙira a harkokin watsa labarai

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Minista ya yaba wa NBTE kan bunƙasa ƙwarewar ƙirƙira a harkokin watsa labarai

Minista ya yaba wa NBTE kan bunƙasa ƙwarewar ƙirƙira a harkokin watsa labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!