• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tattalin Arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23% a zango na biyu na 2025 – NBS

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 22, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tattalin Arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23% a zango na biyu na 2025 – NBS
Manoma a cikin farin ciki

Manoma a cikin farin ciki

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar 2025 idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Nijeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja a ranar Litinin.

Rahoton ya nuna cewa wannan cigaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025.

A cewar rahoton, ɓangaren noma ya samu ci gaban kashi 2.82 idan aka kwatanta da kashi 2.60 da aka samu a zango na biyu na 2024.

Ɓangaren masana’antu ya samu cigaban kashi 7.45, wanda ya ninka kashi 3.72 da aka samu a zango na biyu na 2024.

Ɓangaren ayyuka kuma ya samu kashi 3.94 idan aka kwatanta da 3.83 na zango na biyu na 2024.

Rahoton ya ce a cikin zango na biyu na 2025, darajar GDP ta kai naira tiriliyan 100.73, idan aka kwatanta da naira tiriliyan 84.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, wanda ya nuna ci gaban shekara zuwa shekara da kashi 19.23.

Haka kuma, ɓangaren mai ya samu ƙarin kashi 6.01 a zango na biyu na 2025 idan aka kwatanta da zangon farko na 2025.

Ɓangaren ya bayar da gudunmawar kashi 4.05 cikin ɗari ga GDP, idan aka kwatanta da kashi 3.51 na zango na biyu na 2024 da kuma 3.97 na zangon farko na 2025.

Rahoton ya kuma nuna cewa matsakaicin adadin fitar da man fetur ya kai ganga miliyan 1.68 a kullum a zango na biyu na 2025, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.41 da aka samu a zango na biyu na 2024, da kuma ganga miliyan 1.62 a zangon farko na 2025.

Previous Post

UNGA: Shettima ya sauka a New York

Next Post

UNGA: Shettima ya tallata damar zuba jari na dala biliyan 200 a fannin makamashi a Nijeriya

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
UNGA: Shettima ya tallata damar zuba jari na dala biliyan 200 a fannin makamashi a Nijeriya

UNGA: Shettima ya tallata damar zuba jari na dala biliyan 200 a fannin makamashi a Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!