Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri na horas da matasa fiye da 260,000 a fannonin sana’o’in dogaro da kai a faɗin ƙasar nan, ƙarƙashin shirin Technical and Vocational Education and Training (TVET).
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, shi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da yake duba wasu cibiyoyin gudanar da shirin a birnin Abuja.
A cewar sa, gwamnati na da burin horas da sama da matasa 900,000 a matakai daban-daban na wannan shiri domin ba su damar samun ƙwarewa da za ta ba su ikon dogaro da kan su tare da inganta tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce: “Muna da cibiyoyi sama da 2,600 a fadin kasar nan. Wannan mataki na farko zai kunshi mutum 260,000, kuma mataki na gaba zai ƙara kusantar da mu burin horas da mutum 960,000.”
Alausa ya ƙara da cewa shirin yana gudana a dukkan jihohin ƙasar nan da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya.
Ya kuma tabbatar wa da mahalarta cewa za su samu kuɗin tallafi da kayan farawa bayan kammala horo, domin su kafa ƙananan sana’o’in su.
Ministan ya bayyana shirin a matsayin wani ɓangare na hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen farfaɗo da ilimin sana’a da kuma ƙarfafa tsarin TVET a matsayin ginshiƙin ilimin ƙasar nan.
Ya ce Shugaban Ƙasa ya amince da ware kashi 5% na kasafin TETFund domin tallafa wa cigaban shirin TVET a duk shekara, abin da ya bayyana a matsayin matakin ɗorewar shirin.
An kaddamar da shirin TVET tun a watan Yuni, a matsayin wani ɓangare na yunƙurin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa ilimin sana’o’i da haɓaka damar aikin yi ga matasa.
Shirin, wanda zai ɗauki lokaci tsakanin watanni shida zuwa goma sha biyu bisa ga irin sana’ar, ya ƙunshi fannonin kiwon dabbobi, kiwon kifi, ƙera tukwane na zamani, da sauran sana’o’in hannu.
A halin yanzu, ana gudanar da horon ne a cikin cibiyoyi sama da 2,600 a faɗin Nijeriya.







