Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’ummomin Musulmi da Kirista a Nijeriya da su yi amfani da watan Ramadan mai alfarma wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna domin cigaban ƙasa.
A cikin saƙon da ya fitar a yau Laraba a Abuja, Shugaban ya bayyana cewa fara azumin Ramadan da na Lent a rana ɗaya a bana wata dama ce ta musamman ga ‘yan Nijeriya su ƙara danƙon zumunci da haɗin kai duk da bambancin addini.
Ya ce watan Ramadan lokaci ne na ibada, sadaukarwa da kyautata wa juna, wanda ya kamata a yi amfani da shi wajen gina zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin kyautata hulɗa tsakanin mabambantan addinai, taimaka wa marasa galihu, guje wa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kai da yin addu’o’i domin tsaro da cigaban ƙasa
Ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi rayuwa bisa kyawawan koyarwar addinan su tare da nuna tausayi da haƙuri ga juna, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙan cigaban kowace al’umma.
Shugaban ya kuma yi addu’ar cewa albarkar watan Ramadan za a kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba a Nijeriya.







