Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura sababbin jakadu 65 na Nijeriya zuwa ƙasashe daban-daban na duniya da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Juma’a ta bayyana cewa jakadun sun haɗa da ma’aikatan diflomasiyya 31 (career ambassadors) da kuma waɗanda ba ma’aikatan diflomasiyya ba 34 (non-career ambassadors).
Majalisar Dattawa ta riga ta tabbatar da sunayen jakadun a watan Disambar bara.
Daga cikin waɗanda aka tura akwai:
Sanata Grace Bent – Jakadiya a Lome, Togo
Sanata Ita Enang – Jakada a Afrika ta Kudu
Victor Ikpeazu – Spain
Nkechi Linda Ufochukwu – Tel Aviv, Isra’ila
Mahmud Yakubu – Ƙatar
Reno Omokri – Meziko
Aminu Dalhatu – Babban Kwamishina a Birtaniya
Janar Abdulrahman Bello Dambazau (mai ritaya) – Chana
Lateef Kayode Are – Amurka
Femi Fani-Kayode – Jamus
Yakubu N. Gambo – Saudiyya
Jimoh Ibrahim – Babban Wakilin Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.
A ɓangaren jakadu ma’aikatan diflomasiyya kuwa, gwamnati ta tura su zuwa ƙasashe daban-daban ciki har da:
Mohammed Mahmud Lele – Aljeriya
Ahmed Mohammed Monguno – Masar
Muhammad Saidu Dahiru – Indiya
Abdussalam Habu Zayyad – Senegal
Shehu Ilu Barde – Ghana
Aminu Nasir – Itofiya
Haidara Mohammed Idris – Nezalands
Bako Adamu Umar – Marokko
Sulu Gambari Olatunji Ahmed – Maleshiya
Ibrahim Danlami – Kenya
Adebayo Emmanuel Ayeni – Beljiyam
Wahab Adekola Akande – Siwizaland
Bello Dogon-Daji Haliru – Thailand, da sauran su.
Sanarwar ta ƙara da cewa Birtaniya ta riga ta bayar da amincewar diflomasiyya (agreement) ga Babban Kwamishinan Nijeriya mai jiran gado, Aminu Ɗalhatu.
Haka kuma Faransa ta amince da Ayo Oke a matsayin jakaden Nijeriya a ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta ba da sanarwar sauran ƙasashen da aka tura jakadun, tare da neman amincewar su kamar yadda tsarin diflomasiyya ya tanada.
Tinubu ya kuma umurci ma’aikatar da ta gaggauta shirya shirin horaswa ga dukkan jakadun kafin su kama aiki a ofisoshin jakadancin Nijeriya a faɗin duniya.







