Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Yusuf Abba, ya sake jaddada ƙudirin hukumar na ƙara inganta yadda ake gudanar da ayyukan hidima ga alhazai ta hanyar daidaita ayyukan ta da kamfanin da ke ba ta hidima, domin kauce wa matsalolin da aka fuskanta a shekarar 2025.
Wata sanarwa da aka fitar daga hukumar a yau, ɗauke da sa-hannun Shafi’i Sani Mohammed, ta ce shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron dabaru da jami’an kamfanin Mashariq Aldhahabiya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Daraktocin sa, Mohammed Amin Hassan Andangiri.
Kamfanin, mai hedikwata a Saudiyya, shi ne zai kula da dukkan ayyukan hidima da za a bai wa alhazan Nijeriya da ke tafiya ƙarƙashin kujerun gwamnati a Masarautar Saudiyya.

Ambasada Abba ya ce an koyi darasi daga matsalolin da aka samu a aikin da ya gabata, kamar rashin daidaiton bayanai tsakanin jerin sunayen fasinjojin jirage (manifest), lambobin kwangila da kuma rabon masaukai, wanda ya kawo cikas ga tafiyar da alhazai cikin sauƙi.
Ɓangarorin biyu sun amince da bai wa batutuwa kamar bin ƙa’idojin lokacin fitar da biza, ɗora sahihan bayanai cikin tsarin kwamfuta, da kuma tabbatar da ingancin kwangilar masauki kafin tashi zuwa Saudiyya muhimmanci.
Haka kuma, NAHCON za ta ƙara tsaurara duba bin ƙa’idoji a cibiyoyin tashi domin tabbatar da cewa jerin sunayen fasinjoji da rabon gidajen masauki sun yi daidai da bayanan da aka amince da su.
An kuma amince da samar da ofishin kula da halin da ake ciki (Situation Room) na haɗin gwiwa domin samar da sababbin bayanai a ainihin lokaci da kuma magance matsalolin aiki cikin gaggawa.
Hukumar ta ce wannan ganawar na daga cikin manyan dabarun NAHCON na tabbatar da gudanar da aikin Hajjin alhazan Nijeriya cikin sauƙi da tsari. (NAHCON)







